Cika shekaru 76: Wasu muhimman abubuwa 7 a kan Buhari

Cika shekaru 76: Wasu muhimman abubuwa 7 a kan Buhari

A yau, Litinin 17 ga watan Disamba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru 76 da haihuwa. Mafi yawancin mutane sun san shi a matsayin shugaban Najeriya amma akwai wasu muhimman abubuwa da kowa ya sani game da shugaban kasar ba.

Ga jerin wasu muhimman abubuwa 7 game da shugaba Muhammadu Buhari:

Cika shekaru 76: Wasu muhimman abubuwa 7 a kan Buhari

Cika shekaru 76: Wasu muhimman abubuwa 7 a kan Buhari
Source: Twitter

1. Shugaba Buhari ne da na 23 a gidansu

Shugaba Muhammadu Buhari ne da na 23 a wajen mahaifinsa. Wannan na nuna cewa yana da 'yan uwa 22. An haifi shugaban kasar ne a shekarar 1942.

2. Mahaifin Buhari ya rasu lokacin yana da shekaru 4 a duniya

Mahaifinsa ya rasu a lokacin yana kankanin yaro dan shekaru hudu a duniya amma cikin ikon Allah ya rayu ya zama babban mutum mai daraja da kima a idon duniya kamar yadda muka sani.

3. Ya shiga soja yana da shekaru 19 a duniya

Saboda kishin kasarsa da sha'awar yiwa kasa hidima, shugaba Muhmmadu Buhari ya shiga aikin soja a lokacin yana matashi dan shekara 19 da haihuwa.

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

4. Buhari yana da shekaru 43 a lokacin da ya zama gwamnan tsohuwar Arewa maso gabas

An nada Shugaba Muhammadu Buhari gwamnan tsohuwar jihar Arewa maso gabas yana da shekaru 43 a duniya. Arewa maso gabas a wancan lokaci yana da jihohi da dama a karkashinsa. Ya kuma mulki jihar Borno na yanzu na kankanin lokaci a baya.

5. Buhari ya yi takarar sau 3 kafin ya yi nasara a 2015

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi takarar shugabancin kasa sau uku kafin daga bisani ya yi nasarar lashe zaben a shekarar 2015. Wannan na nuna cewa shi mutum ne mai hakuri da cijewa kan abinda ya sanya a gaba.

6. Buhari ya yi aure sau biyu

Shin ko kun san cewa Aisha Buhari ba itace matar Buhari ta farko ba? Buhari ya fara auren matarsa na farko mai suna Safinatu a shekarar 1985 wadda ta haifa masa yara 5 kafin suka rabu. Daga bisani ya auri Aisha itama ta haifa masa yara biyar. Cikin yaransa 10, Allah ya yiwa biyu rasuwa.

7. Buhari ya samu lambobin yabo daga kasashen duniya

Shugaba Muhammadu Buhari ya samu lambar yabo na girmamawa daga kasashen duniya daban-daban. Cikin kasashen da suka baiwa Buhari lambar yabo akwai kasar Congo da Equitorial Guinea.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel