Abun Bakin Ciki
Da yake bayyana abinda ya faru gare shi, Urhoghide, ya ce "dama na san sun shirya ci min mutunci tun kafin na bar Abuja. Bayan na sauka sai kwamishinan 'yan sanda ya bani shawarar na jira gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki kuma nay
Bayan labari ya isa hukumar Hisbah ne sai ta tura jami'an ta domin su sare bishiyar saboda barazana da illar da take da ita ga imanin musulmi. Sai dai an yi dauki ba dadi da matasan dake karbar kudi a wurin bishiyar da jami'an His
An tabbatar da kimanin rayuka 12 sun salwanta tare da raunatar mutane 5 a wani mummunan hatsarin motoci biyu kirar Volvo da Ford da ya afku a yankin Foursquare dake babbar hanyar Legas da Ibadan a ranar Asabar din da ta gabata.
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yi nasarar cafke wani dan Boko Haram da ake zargi da kitsa makirci wajen shirya mafi akasarin hare-haren da suka afku a jihar Benuwe.
Wata matar aure Sandra Ekpa, ta roki babbar kotun garin Mararaba a jihar Nasarawa akan ta raba tsohon auren ta da ta yi shekaru uku da suka gabata a sanadiyar mai gidan ta da ya kauracewa kwanciya da ita gami da aikata tsubbu.
NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, wannan matashi ya sha yunkurin kashe kansa da diddikar guba har a karo uku inda ake takar sa'a 'yan uwan sa ke hana shi. An tsinto gawar Kawa ne rataye a daren ranar 24 ga watan Afrilu a gidan su.
Shugaban jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, Najeriya da sauran kasashen duniya su na ci gaba da zuba idanu a yayin da romon dimokuradiyya da ya kamata su kwankwada ke ci gaba da zagwanyewa sakamakon rashin kulawar gwamnatin kasar nan.
Kakakin ya ce 'yan Achabar sun yi dandazo tare rufe jami'in da duka har ta kai ga sun yi masa rauni. Ya kara da cewar lamarin kan iya fin haka tsamari ba don jama'a dake wucewa sun kwaci VIO din ba. Yanzu haka an kai Mista Eyge as
Da yake bayar da ba'asin abinda ya faru, Bello, ya ce ya kashe dan uwansa Abdullahi ne bayan barkewar rikici a kan wata saniya da suka tsinta kuma aka bashi ya je ya sayar da ita amma sai ta gudu. Ya cigaba da cewa bayan ya sanar
Abun Bakin Ciki
Samu kari