Amurka Ta Samu Nasara Mafi Girma cikin Shekaru 25 a Farmakin da Ta Kawo Najeriya

Amurka Ta Samu Nasara Mafi Girma cikin Shekaru 25 a Farmakin da Ta Kawo Najeriya

  • Gwamnatin Amurka ta sake fito da nasarorin da ta samu a hare-haren hadin gwiwa da ta kawo Najeriya domin kawo karshen ayyukan ta'addanci
  • Wani hadimin shugaban Amurka, Sebastian Gorka ya ce dakarun kasar sun halaka 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi 199 a hari daya kacal
  • Gorka ya ce wannan shi ne mafi girman adadin mayakan kungiyar ta'addanci da aka kashe a farmaki guda tun bayan harin 11 ga Satumba, 2001

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Mataimakin mai ba Shugaban Amurka Donald Trump shawara kuma babban daraktan yaƙi da ta’addanci a Kwamitin Tsaron Ƙasa, Sebastian Gorka, ya yi magana kan hare-haren da aka kawo Najeriya.

Sebastian Gorka ya ce dakarun ƙasar Amurka sun kashe mayaka 199 na kungiyoyi ta'addanci a farmaki guda da aka gudanar a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwan fashewa sun tashi da sojan Isra'ila a Lebanon

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana gaisWa da dakarun sojoji a birnin Washington Hoto: Donald J. Trump
Source: Twitter

Gorka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Marissa Streit, wadda aka fitar a ranar 24 ga Yuni, 2026, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da yake magana kan yaƙin da Amurka ke yi da ta’addanci, Gorka ya ce gwamnatin Trump tana ci gaba da samun nasara kan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini.

"Idan kuna barazana ga Amurkawa ko kuna kai hari kan Kiristoci saboda addininsu, shugaban kasa zai aika muku da saƙo mai ƙarfi," in ji shi.

Amurka ta samu nasara mafi girma

A cewarsa, kimanin makonni uku kafin wannan hira, ya kalli yadda jami'an Amurka suka kashe mayakan jihadi 199 a wani farmaki da aka gudanar a Najeriya.

"Na kalli abin kai tsaye daga Situation Room. Mun kashe mayakan jihadi 199 a aiki guda a Najeriya."

Gorka ya ce wannan shi ne mafi girman adadin mayakan da aka kashe a aiki guda tun bayan harin 11 ga Satumba, 2001.

Kara karanta wannan

Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu

Sai dai bai fayyace ko yana magana ne kan farmakin haɗin gwiwar Amurka da Najeriya na ranar 15 ga Mayu, wanda aka ce ya kashe Abu-Bilal al-Minuki, ko kuma farmakin ranar 30 ga Mayu da aka ruwaito cewa ya kashe mayaƙan ISWAP 21 ba.

Dalilin Amurka na kwo dauki Afirka

Gorka ya kuma bayyana cewa an kwaso dimbin kayayyaki daga sansanonin mayaƙan da aka kai wa hari, inda ya ce sai da aka buƙaci ƙarin jirgin sama domin ɗauko kayan saboda yawansu.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka fi mayar da hankali kan Afirka wajen yaƙi da ta’addanci, Gorka ya ce karuwar yawan Kiristoci a nahiyar na daga cikin dalilan da suka sa ƙungiyoyin jihadi ke kai hare-hare a yankin.

Shugaba Tinubu.
Mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeria Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya kuma ce ƙungiyar ISIS ta yi amfani da raunin tsarin mulki da rikice-rikicen da ke yankin Sahel wajen faɗaɗa ayyukanta da yaɗa manufarta, kamar yadda Premium Times ta rahoto

Jarumin Nollywood ya zama sojan Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen jarumin masana'antar fina-finan Nollywood ta Najeriya, Joseph Momodu ya sanar da shiga rundunar sojin Amurka.

Kara karanta wannan

Kazamar fada ta barke tsakanin kwamandojin ISWAP, an kashe 'yan ta'adda da dama

Jarumin ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasara da kuma cikar burin da ya gada daga marigayi mahaifinsa.

Momodu ya bayyana cewa shiga rundunar sojin Amurka na da muhimmanci a gare shi saboda ya ci gaba da abin da marigayi mahaifinsa ya fara

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262