Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya

Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya

Gwamnati da al'ummar Najeriya na cigaba da kara nuna damuwar su a kan yawaitar amfani da maganin tari mai saka maye da ake fi sani da kodin.

A yayin zaman majalisar dattijai na yau, shugaban masu rinjaye a majalisar, Ahmed Lawan, ya bayyana cewar kusan kashi 70% na sindarin kodin din da ake shigowa da shi kasar nan na karewa ne a dajin Sambisa.

A cewar Sanata Lawan, "yanzu a Najeriya zai yi wuya ka samu wani gida da babu mai amfani da wani abun maye. Babu wani abu dake barazana ga rayuwar jama'a a Najeriya bayan kungiyar Boko Haram kamar amfani da sinadarin kodin.

Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya
Kashi 70% na kodin din dake Najeriya a dajin Sambisa ake shanye shi - Sanatan Najeriya

"A bayanin da nake samu da safiyar yau, kashi 70% na kodin din ake shigowa da shi arewacin Najeriya na karewa ne a dajin Sambisa, sansanin 'yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram. Lallai akwai bukatar mu tashi tsaye wajen daukan mataki domin dakile shigowa tare da sarrafa maganin tari mai dauke da sinadarin kodin," in ji Sanata Lawan.

Rahotanni jami'an tsaro ya sha bayyana cewar ana samun kwayoyi dake gusar da hankali a yawancin sansanin 'yan Boko Haram.

DUBA WANNAN: Bayan ya yi burus da majalisar dattijai, Sifeton 'yan sanda ya ziyarci El-Rufa'i, duba hotunan su:

A jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da haramta sarrafa maganin tari mai dauke da sinadarin kodin a Najeriya.

Majalisar tayi alkawarin hada kai da gwamnatin tarayya domin ganin an dakile duk wasu hanyoyi da sinadarin kodin ke shiga hannun jama'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng