Badakalar Biliyoyi: EFCC Ta Gurfanar da Tsofaffin Shugabannin Matatun Man Najeriya
- EFCC ta gurfanar da tsofaffin shugabannin PHRC da WRPC kan zargin karkatar da kudaden gyaran matatun man fetur da halasta kudaden haram
- Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta shigar da tuhume-tuhume 12 kan Ahmed Dikko da kuma 8 kan Jimoh Yisawu a wata kotun Abuja
- Binciken hukumar EFCC ya shafi gyaran matatun mai, inda aka ce an kwato biliyoyin naira da miliyoyin daloli daga 'masu handamar'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban matatar man Fatakwal (PHRC), Ahmed Adamu Dikko, da tsohon takwaransa na matatar man Sinadaran Warri (WRPC), Jimoh Olasunkanmi Yisawu.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta gurfabar da mutanen biyu ne kan zargin halasta kudaden haram da suka shafi kudaden gyaran matatun mai na Najeriya.

Source: Facebook
An gurfanar da tsofaffin shugabannin matatu
Takardun kotu sun nuna cewa EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 12 kan Dikko da kuma tuhume-tuhume 8 kan Yisawu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar 22 ga Yuni, in ji rahoton Premium Times.
EFCC ta zargi tsoffin shugabannin matatun biyu da amfani da mukamansu wajen karkatar da kudade, karbar kudade daga ‘yan kwangilar da ke aiki da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), da kuma gudanar da wasu asusun banki da ake zargin an yi amfani da su wajen boye kudaden da ba su dace ba.
Hukumar ta ce wasu daga cikin laifukan sun sabawa dokar hana halasta kudaden haram ta shekarar 2022.
Wannan mataki na zuwa ne a cikin babban binciken EFCC kan shirin gyaran manyan matatun man fetur na Najeriya da aka kashe makudan kudade a kai.
A baya, an ruwaito cewa hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 9.4, dala miliyan 21.2 da kuma wasu kadarori a wani bangare na binciken karkatar da kudaden gyaran matatun.
Bisa farashin canjin Babban Bankin Najeriya (CBN) na N1,380 kan dala daya, kudin dala miliyan 21.2 sun kai kusan Naira biliyan 29.26, wanda ya kawo jimillar kudaden da aka kwato zuwa kusan Naira biliyan 38.66.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Ahmed Dikko
A cewar takardar tuhuma, EFCC ta zargi Ahmed Dikko da yin wasu hada-hadar kudi da ake danganta su da kudaden da aka samu daga ayyukan gyaran matatar Port Harcourt.
Daga cikin zargin akwai cewa a watan Fabrairun 2024, yayin da yake matsayin Manajan Darakta na PHRC, ya biya kimanin Naira miliyan 218.3 domin sayen wata kadara a Abuja ba tare da amfani da banki ba, abin da EFCC ta ce ya saba dokar hana halasta kudade.
Hukumar ta kuma zarge shi da rike Naira miliyan 100 da ake zargin wani kamfanin kwangila mai suna Ebenco Global Link Limited ya biya masa.
Sauran zarge-zargen sun hada da:
- Rike Naira miliyan 90 daga wata mu’amala da Ebenco Global Link Limited.
- Boye asalin wasu Naira miliyan 90 ta hanyar wani asusun banki.
- Karbar Naira miliyan 30 daga wani kamfani mai suna Ebenco Enterprises.
- Karbar wasu kudade daga Dogai Global Resources da Gasontex Limited.
EFCC ta kuma zargi Dikko da boye asalin Naira miliyan 328.71 da ake cewa an biya ta hannun Masterpiece Projects & Investment Limited.
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Jimoh Yisawu
A bangaren tsohon shugaban WRPC, Jimoh Yisawu, EFCC ta zarge shi da halasta makudan kudade ta hannun wasu mutane da kuma yin manyan hada-hadar kudi ba tare da bin ka’ida ba.
Hukumar ta ce tsakanin Oktoban 2023 zuwa Mayun 2025, Yisawu ya canza dala 789,950 ta hannun wani mutum mai suna Samaila Bala, kudin da ake zargin ba su dace da kudin shigar sa na halal ba.
An kuma zarge shi da yin wasu manyan biyan kudi ta tsabar kudi ba tare da amfani da cibiyoyin kudi ba.
Sauran zarge-zargen sun hada da karbar:
- Naira miliyan 25.56 daga kamfanin JKpeez Impex Co.
- Tura Naira miliyan 65.86 zuwa Cordros Securities Limited domin sayen Treasury Bills.
- Rike Naira miliyan 15 da ake zargin Ebenco Global Link Limited ya biya.
- Rike karin Naira miliyan 3 daga wannan kamfani.
Asali: Legit.ng


