Mayakan kungiyar Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri zuwa kano

Mayakan kungiyar Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri zuwa kano

Rahotanni da muke samu daga wata majiya daga jihar Borno na nuni da cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun tare babbar hanyar zuwa Kano daga Maiduguri.

Motoci dake tahowa daga Maiduguri na juyawa daga garin Auno inda mayakan suka datse suke ta barin wuta'

Mayakan kungiyar Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri zuwa kano
Mayakan kungiyar Boko Haram sun tare hanyar Maiduguri zuwa kano

Wata majiyar soji ta sanar da jaridar Vanguard cewer mayakan sun kutso ta cikin garin na Auno cikin motocin yaki, motocin hawa da babura masu kafa uku.

DUBA WANNAN: Matasa biyar a jihar Benuwe sun samu aikin soja kyauta, karanta bajintar da suka yi

Saiudai dakarun sojin Najriya sun mayar da martani ta hanyar tunkarar mayakan domin fatattakar su daga kan hanyar.

Ya zuwa yanzu babu wani rahoto daga hukumar sojin Najeriya dangane da abinda ke faruwa. Kazalika babu rahoton adadin mutanen da suka rasa rai ko samun rauni sakamakon harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel