Kungiyar Obidient Ta Bada Tabbaci kan Takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da Hukuncin Kotu

Kungiyar Obidient Ta Bada Tabbaci kan Takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da Hukuncin Kotu

  • Kungiyar Movement ta yi martani bayan kotu ta soke hukuncin da ya tilastawa hukumar zabe ta INEC yin rajista ga jam'iyyar NDC
  • Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Yunusa Tanko, ya bayyana cewa Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso za su kasance a zaben 2027
  • Yunusa Tanko ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta girmama 'yancin bangaren shari'a na kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Obidient Movement ta yi magana kan takarar Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaben 2027.

Kungiyar ta tabbatarwa masu goyon bayanta cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, za su kasance a kan takardar kada ƙuri'a a babban zaɓen shekarar 2027.

Obidient ta ce Kwankwaso da Obi za su yi takara
Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce shugaban ƙungiyar na ƙasa , Dr. Yunusa Tanko, ya ba da wannan tabbacin ne yayin wani taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Litinin, 29 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

2027: An miƙa bukata ga Kwankwaso da Obi bayan an fara jita jitar za su fice daga NDC

Me Obidient ta ce kan hukuncin kotu?

Yunusa Tanko ya yi watsi da fargabar cewa abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa da shari'a na kwanan nan za su iya gurgunta haɗin gwiwar 'yan adawa.

Tanko yana mayar da martani ne ga hukuncin da mai shari'a Isah Dashen ya yanke wanda ya soke hukuncin kotu na ranar 10 ga watan Disamba, 2025, wanda ya umarci hukumar zabe ta INEC da ta yi rajistar NDC a matsayin jam'iyyar siyasa.

Yayin da yake sake ba wa magoya bayan na Obidient kwarin gwiwa, Tanko ya jaddada cewa haɗin gwiwar da ake ginawa a kewayen Obi da Kwankwaso yana nan da ƙarfi kuma ba zai raunana ba sakamakon yunkurin kawo masa cikas.

An bada tabbaci kan Obi da Kwankwaso

"Muna son sake tabbatar wa masu goyon bayanmu cewa haɗin gwiwarmu yana nan daram kuma yana ƙara yin ƙarfi. Peter Obi da Dr. Rabiu Kwankwaso za su kasance a kan takardar zaɓe a 2027. Babu wani adadin tsoratarwa ko dabarun shari'a da zai iya dakatar da nufin al'umma.”

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zargin ana shirya masu gadar zare, za a hana ADC shiga zaben 2027

- Yunusa Tanko

Yunusa Tanko ya lura cewa ƙungiyar tana da masaniya kan damuwar da ake da ita daga hukuncin kotun, da kuma takaddamar siyasa, amma ya nuna cewa 'yan adawa za su ci gaba da bin manufofinsu ta hanyoyin doka da na zaman lafiya.

A cewarsa, haɗin gwiwar ya ƙuduri aniyar samar wa 'yan Najeriya wata mafita ta daban ga jam'iyya mai mulki, jaridar Tribune ta kawo labarin.

Kwankwaso da Peter Obi za su yi takara a zaben 2027
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi a wurin taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

An yi kira ga gwamnatin tarayya

Ya yi kira ga magoya baya da su kwantar da hankulansu, su kasance cikin haɗin kai, kuma su sadaukar da kansu ga tsarin dimokiraɗiyya, inda ya ƙara da cewa ƙungiyar za tana ci gaba da kare haƙƙoƙin shugabanninta da na mambobinta.

Tanko ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran 'yan siyasa da su girmama 'yancin ɓangaren shari'a kuma su bar tsarin zaɓe ya kasance cikin 'yanci da adalci.

Abin da Kwankwaso ya ce kan shari'ar NDC

Kara karanta wannan

Abin da sabuwar dokar kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya ta kunsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan shari'ar da jam'iyyar ke fuskanta.

Tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2023, ya tabbatar wa magoya bayansu cewa za a shawo kan matsalolin shari'a da suke fuskanta.

Kwankwaso ya bukaci dukkannin 'yan jam'iyya da magoya bayan NDC da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa duk da kalubalen da ake fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng