Yadda wata Budurwa ta yanke mazakutan Saurayinta da almakashi bayan ya fitar da bidiyon kwanciyarsu
Wata mata yar asalin kasar Ajantina ya guntule mazakutan saurayinta sakamaton bata mata rai da yayi, bayan ta fitar da bidiyon kwanciyarsu a tare ga abokansa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Buduwar mai shekaru 26, Baratti ta tafka wannan laifi ne a watan Nuwambar bara, a unguwar Nueva Cordoba dake garin Cordoba na jihar Ajantina, inda ya jefa rayuwar saurayinta mai shekaru 40, Sergio Fernandes cikin matsanancin hali, bayan ta guntule kasha 95 na gabansa.
KU KARANTA: Rikicin BokoHaram: Obama bai baiwa Najeriya kyakkyawar gudunmuwar da muke bukata ba – Garba Shehu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Baratti ta ce ta shiga mawyacin hali bayan saurayin ta fitar da wannan bidiyon, don haka ta yi amfani da almakashi ta yanke masa gaba. Sai dai a yanzu haka tana daure a Kurkuku zuwa lokacin da za’a kammala shari’arta.
“Ni na yanke masa mazakuta, amma ba duk ba, rauni ne na ji masa.” Inji ta, a wani hira da ta yi da manema labaru. Shi kuwa lauyan Sergio yace a yanzu haka yana cikin mawuyacin hali,kuma yana jira sabon tiyata da za’a yi masa.
Sai dai likitoci da ma’aikatan jinya na Asibitin da Fernandez ke jinya sun bayyana cewar sun gagara mayar da sashin mazakutar, don haka zasu jira zuwa wani lokaci da za’a yi masa tiyata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng