An Kama Mutum 10 kan Kashe Shugaban Miyetti Allah a Benue
- Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban Miyetti Allah, Alhaji Ardo Risku Muhammad
- An kama waɗanda ake zargin ne bayan cikakken binciken sirri da sintiri na musamman da aka ƙaddamar bayan kashe shugaban Fulani
- Kwamishinan ‘yan sandan Benue ya ce ana cigaba da bincike domin ganowa da kama sauran mutanen da ake zargi da kashe Ardo Risku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN na jihar, Alhaji Ardo Risku Mohammed da abokinsa Yakubu Isa.
An kama waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da binciken sirri mai zurfi da kuma ayyukan sintiri na musamman da aka fara bayan da aka yi wa mutanen biyu kwanton ɓauna tare da kashe su yayin da suke dawowa daga wani taron zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da kama mutanen da ake zargin ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.
Ardo Risku: An kama mutum 10
Da yake tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya ce rundunar ta samu gagarumar nasara wajen gano waɗanda ke da hannu a harin.
A cewar sanarwar, mutanen da aka kama sun haɗa da Titus Thyodenda mai shekara 25; Utibe Sam mai shekara 20; Owoicho Ameh mai shekara 18; Sunday Useni mai shekara 21; Sunday Ogbanje mai shekara 46.
Sauran sun hada da Daniel Raphael mai shekara 23; Adokole John mai shekara 24; Samuel Ogazi mai shekara 32; Agbo Daniel mai shekara 25; da Onazi James mai shekara 30.
Bayanin kwamishinan 'yan sanda
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Benue, CP Cletus Nwadiogbu, ya yaba wa jami’an sintiri da masu bincike kan matakan gaggawa da suka dauka, yana mai bayyana kamen a matsayin babban ci gaba a binciken da ake yi.
“Rundunar ta samu gagarumar nasara a binciken da ake yi. Ya zuwa yanzu an kama mutum 10 da ake zargi da hannu a lamarin bayan gudanar da binciken sirri da ayyukan sintiri na musamman,”
In ji kwamishinan.
Ya tabbatar wa jama’a cewa bincike na ci gaba, kuma an ƙara ƙaimi wajen ganowa, bibiya da kama sauran mutanen da ake zargin suna da alaƙa da kisan.
“Rundunar ta jajirce wajen tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban shari’a bisa tanadin doka,”
In ji shi.

Source: Original
Kiran kwamishinan ga jama'a
CP Nwadiogbu ya buƙaci mazauna jihar su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa bincike da sauran ayyukan tsaro a faɗin jihar.
Leadership ta rahoto cewa ya sake jaddada ƙudirin rundunar ‘yan sandan Jihar Benue na kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaron jama’a a duk faɗin jihar.
An harbe 'yan bindiga a Benue
A wani rahoto, kun ji cewa dakarun Najeriya sun yi artabu da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne a wani yanki na jihar Benue.
Musayar wutar da suka yi ta jawo kashe mutane biyu daga cikin 'yan ta'addan da ake zargin sun nufi wata kasuwar doya.
Sojoji sun yi nasarar kwato makamai da suka haɗa da bindiga kirar AK-47 da wasu kayayyaki da dama a hannun mutanen.
Asali: Legit.ng
