An Tafka Babban Rashi: Mahaifiyar Sakataren APC na Kasa Ta Bar Duniya
- Sakataren jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tafka babban rashi na mahaifiyarsa bayan fama da jinya
- Jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta mika sakon ta'aziyya ga Sanata Ajibola Basiru bayan rashin mahaifiyar ta sa
- APC ta ce rasuwar marigayiyar hukuncin Allah ce, tare da yabon rayuwarta mai cike da tawali'u, kyautatawa, tarbiyya da bautar Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya reshen Osun ta yi jimami kan rashin da aka yi a jihar.
An tabbatar da cewa mahaifiyar sakataren jam'iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, Hajiya Sidikat Basiru, ta rasu.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da shi kansa sakataren APC, Ajibola Basiru ya wallafa a shafinsa na X a yau Lahadi 28 ga watan Yunin 2026.
APC reshen Osun ta sanar da rasuwar tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalanta da sauran yan uwa da abokan arziki.
An yi rashin mahaifiyar sakataren APC
Sanarwar ta bayyana cewa rasuwar Hajiya Sidikat Basiru babban rashi ne ga iyalanta da duk wadanda suka amfana.
Jam'iyyar ta ce rasuwar marigayiyar ta zo ne bisa nufin Allah Madaukakin Sarki, wanda Shi ke ba da rai kuma Ya karbe shi lokacin da Ya tsara.
APC ta bukaci iyalan mamaciyar su karbi kaddarar Allah cikin imani, hakuri da yarda, tana mai cewa mutuwa wajibi ce ga kowace rayuwa.
Jam'iyyar ta bayyana cewa rasuwar uwa mai kulawa da kuma jagorar iyali na barin babban gibi wanda ba zai taba cika ba.
Olabisi ya bayyana marigayiya a matsayin mace ta gari mai cike da tawali'u, kyautatawa, tarbiyya mai kyau da sadaukarwa wajen bautar Allah da hidimar bil'adama.
Jam'iyyar APC ta ce tana tare da Sanata Basiru a wannan lokaci na alhini, tana fahimtar irin radadin da rasa uwa ke haifarwa ga 'ya'ya da iyali.

Source: Original
Addu'ar da APC ta yi wa marigayiywar
Jam'iyyar ta yi addu'ar Allah Ya ba Sanata Basiru da 'yan uwansa hakuri, juriya da karfin zuciyar jure wannan babban rashi da suka yi.
Sanarwar ta ce kyakkyawar tarbiyya da dabi'u da marigayiya ta koyar da 'ya'yanta su ne mafi girman abin tunawa da ta bari.
Ta kara da cewa hidimar jama'a da Sanata Basiru ke yi tana nuna irin tarbiyyar kirki da mahaifiyarsa ta dasa masa tun yana karami.
APC ta kuma mika ta'aziyyarta ga daukacin iyalai, dangi da abokan arzikin marigayiyar, tana addu'ar Allah Ya gafarta mata kura-kuranta.
Jam'iyyar ta roki Allah Ya yalwata kabarinta da haske, Ya karbi komawarta gare Shi, tare da shigar da ita Aljannatul Firdausi.
Basiru a magantu kan tasirin APC
A baya, an ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana cewa tasirinta da kuma shririn wasu gwamnonin adawa a Najeriya na sauya sheƙa zuwa cikinta gabanin zaɓen 2027.
Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru ya faɗi hakan a wurin wani taron horarwa da jam'iyyar ta shirya a Abuja.
Ya ce a yanzu APC na da gwamnoni 23 amma akwai wasu da dama da suka nuna sha'awar shiga cikinta nan ba da daɗewa ba.
Asali: Legit.ng

