Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuwar Sufeton 'Yan sanda a jihar Ogun

Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuwar Sufeton 'Yan sanda a jihar Ogun

Wani Sufeton 'yan sanda ya yi gamo da ajali kwatsam sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kauyen Adedero daura da babbar hanyar Kobape ta birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Kakakin hukumar kula da kiyaye gwanon motoci a manyan hanyoyi na jihar, Mista Babatunde Akinbiyi, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya a birnin na Abeokuta.

Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuwar Sufeton 'Yan sanda a jihar Ogun
Wani Hatsarin Mota ya salwantar da rayuwar Sufeton 'Yan sanda a jihar Ogun

Akinbiyi dai ya bayyana cewa, tsautsayi da ba ya wuce ranar sa ne ya sanya kan mota da Sufeton ke tukawa ya kwace inda ta afka cikin daji tare da yin kuli-kulin bura da allan kafura.

KARANTA KUMA: Mafi Karancin Albashi: N66, 500 sun sha gaban jihar Bauchi - Gwamna Abubakar

Legit.ng kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito ta fahimci cewa, wannan hatsari ya afku ne da misalin karfe 11.30 na safiyar yau Talata inda babban jami'in ya riga mu gidan gaskiya.

Kakakin ya kara da cewa, tuni an killace gawar mamacin a babban asibitin jihar Ogun na Ijaye dake birnin Abeokuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng