Tuban Muzuru: Malami Ya Gargadi Gwamnati game da Karban Tuban Yan Bindiga
- Wani malamin addinin Musulunci ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi nesa da kokarin yafe wa dukkanin mutanen da aka kama da laifin ta'addanci
- AbdulRauf Lagbaji, ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa a rika yafe wa 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kotu ta same su da laifi
- Ya ce addinin Musulunci ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi kisan kai da gangan, yana mai cewa bai kamata a rika kallon tubansu da idon rahama ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo – Shugaban gidauniyar At-Tanzil, AbdulRauf Lagbaji, ya bukaci gwamnatocin Najeriya su fara aiwatar da hukuncin kisa ga duk wani ɗan bindiga ko mai garkuwa da mutane da aka samu da laifi a kotu.
Lagbaji ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni, 2026 yayin gabatar da lacca a bikin ranar Ashura da ƙungiyar Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) reshen jihar Ondo ta shirya.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Malamin ya ce addinin Musulunci ya yi tanadin cewa duk wanda aka samu da laifin kisan kai da gangan ya cancanci hukuncin kisa.
Malami ya soki yafe wa yan bindiga
A ruwayar jaridar Punch, AbdulRauf Lagbaji, ya kuma soki shirin sake mayar da masu aikata laifuffuka da suka ce sun tuba cikin al'umma, yana mai cewa hakan babban kuskure ne domin babu tabbacin za su daina aikata miyagun ayyukan.
A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wa kundin tsarin mulki gyara domin a rika aiwatar da hukuncin kisa cikin gaggawa ga masu garkuwa da mutane da aka samu da laifi.
Lagbaji ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da ya tabbatar an aiwatar da hukuncin kisa kan waɗanda aka samu da laifi kan harin cocin Owo da ya faru a shekarar 2022.
Ya ce:
"Lokaci ya yi da gwamnati za ta fara kashe duk wani ɗan bindiga ko mai garkuwa da mutane da aka samu da laifi, domin Alƙur'ani ya bayyana cewa duk wanda ya kashe wani da gangan, shi ma ya cancanci a kashe shi."

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
An gargadi gwamnati kan tuabbun yan bindiga
Lagbaji ya ce a Musulunci, diyar mutumin da aka kashe ta kai darajar raƙuma 100, wadda ya ce a yau ta kai kusan Naira miliyan 200 ga mutum ɗaya.

Source: Original
Ya ce:
"Saboda haka addininmu bai yarda a rika nuna sassauci ga masu kashe mutane ba. Wane dalili ne gwamnati ke da shi na barin masu irin waɗannan munanan laifuka su koma cikin al'umma?"
Ya gargadi gwamnati da kada ta yi kuskuren yarda cewa 'yan bindiga za su tuba da gaske, yana mai cewa idan ta yi haka, Allah ba zai yi mata rangwame ba a Lahira.
'Yan bindiga sun hallaka limami
A baya kun samu rahoton cewa yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai wani mummunan harin ta'addanci a jihar Sakkwato da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda suka yi barna.
Hatsabiban mutanen sun hallaka limami da wasu mutane uku tare da yin garkuwa da wasu daban zuwa cikin daji a yayin harin da ya jefa mutane a cikin mawuyacin hali na firgici da dimuwa a yankin.
Mutanen yankin sun koka da cewa harin ya jefa su cikin tsaro da fargaba inda da dama daga cikinsu suke shirin daina kwana a gari yayin da lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a wasu daga cikin sassan jihar.
Asali: Legit.ng
