RMAFC, NPC: Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 8 a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sababbin kwamishinoni biyu na RMAFC da shida na hukumar kidaya ta kasa bayan amincewar majalisar tarayya
- Rahotanni sun ce sababbin kwamishinonai sun hada da wakilai daga jihohin Bauchi, Kaduna, Ekiti, Zamfara, Kwara, Katsina, Jigawa da Sokoto
- An gudanar da bikin rantsarwar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja kafin Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin kwamishinoni takwas na hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu bayan samun amincewar majalisar tarayya.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a ranar Litinin 29 ga watan Yunin 2026 a dakin taro na majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.

Source: Twitter
Rahoton The Nation ya nuna cewa an rantsar da sababbin kwamishinonin ne kafin shugaban kasa Tinubu ya fara jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Kwamishinonin RMAFC 2 sun fara aiki
Daga cikin wadanda aka rantsar akwai kwamishinoni biyu na hukumar tattara kudaden shiga da rabon kasa (RMAFC), wadanda suka hada da:
- Amina Ibrahim Gamawa daga jihar Bauchi
- Abdullahi Mukhtar daga jihar Kaduna
Sun yi rantsuwar aiki a lokaci guda, inda suka fara gudanar da ayyukansu a matsayin mambobin hukumar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya kafa domin kula da harkokin rabon kudaden kasa.
An rantsar da kwamishinonin NPC 6
Shugaba Tinubu ya kuma rantsar da sabbin kwamishinoni shida na hukumar kidaya ta kasa (NPC), kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.
Sababbin kwamishinonin da shugaban kasar ya rantsar sun hada da:
- Kolawole Oladipupo Alabi – Jihar Ekiti
- Nasiru Mu’azu – Jihar Zamfara
- Dr. Isaka Alada Yahaya – Jihar Kwara
- Prof. Sadiq Isah Radda – Jihar Katsina
- Suleiman Umar – Jihar Jigawa
- Hon. Chiso Abdullahi Dattijo – Jihar Sokoto
Rantsarwar ta gudana kafin taron FEC

Kara karanta wannan
Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya
Bayan kammala bikin rantsarwar, Shugaba Tinubu ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, inda ministoci suka gabatar da takardu kan muhimman manufofin gwamnati da shirye-shirye.
An gudanar da bikin ne tare da halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Source: Twitter
Haka kuma, shugaban ma’aikatan gwamnati na tarayya, Mrs Didi Esther Walson-Jack, ministoci da wasu manyan mataimakan shugaban kasar sun halarci taron.
Rahoto ya nuna cewa wannan zaman majalisar zartarwa ta tarayya na zuwa ne bayan akalla watanni biyu da ba a gudanar da shi ba.
Tinubu ya sauya fasalin NYSC
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da yi wa hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) garambawul bayan shekaru 53 da kafa ta.
Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ayodele Olawande ya bayyana cewa garambawul ɗin zai bai wa gwamnatin tarayya damar tantance manufofi da tsarin gudanar da hukumar NYSC kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya amince.
Asali: Legit.ng
