Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Fiye da Naira Tiriliyan 2, Za a Zuba Manyan Ayyuka a Jihohi 10

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Fiye da Naira Tiriliyan 2, Za a Zuba Manyan Ayyuka a Jihohi 10

  • Gwamnatin tarayya ta amince da ayyukan manyan tituna da za su lakume fiye da Naira tiriliyan 2 a fadin jihohi 10 a Najeriya
  • Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa yau Litinin, 29 ga Yuni, 2026
  • A cewarsa, ayyukan za su haɗa da gina sababbin hanyoyi da kuma gyaran manyan tituna da ke da muhimmanci domin sauƙaƙa zirga-zirga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kashe kimanin Naira tiriliyan 2.078 domin aiwatar da manyan ayyukan gine-gine da gyaran hanyoyi a jihohi 10 na ƙasar nan.

Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa (FEC) da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Litinin.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar zartarwa ta tarayya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jihohi 10 da za su amfana da aikin

Umahi ya ce majalisar ta amince da manyan ayyukan hanyoyi guda 23 da suka shafi jihohin Adamawa, Taraba, Ebonyi, Kwara, Cross River, Kogi, Legas, Neja, Oyo da Filato, cewar rahoton Vanguard.

A cewarsa, ayyukan za su haɗa da gina sababbin hanyoyi da kuma gyaran manyan tituna da ke da muhimmanci domin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci.

An ƙara kuɗin aikin titin Gashua

Ministan ya kuma bayyana cewa FEC ta amince da ware ƙarin kuɗi har Naira biliyan 15 na kwangilar titin Gashua da ke jihar Yobe, wadda aka bayar tun shekarar 2022.

Haka kuma, majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 15.246 domin fara kashi na biyu na aikin titin Yola–Fufore–Gurin, bayan kammala kashi na farko.

Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci ma’aikatar ayyuka da ta fara shirye-shiryen sake gina sassan hanyar da suka lalace ta amfani da tsarin kankare domin ƙara wa hanyar ɗorewa da inganta tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Dangote zai gina hanyoyi a Najeriya

Majalisar ta kuma amince da sake gina kusan kilomita 400.9 na titunan gwamnatin tarayya ta hanyar tsarin haraji na Tax Credit, inda Kamfanin Dangote zai aiwatar da aikin kan kuɗin da ya kai Naira tiriliyan N1.8325.

Umahi ya ce wannan sabon shiri ya maye gurbin wata kwangila da aka bayar a shekarar 2022, kuma ana sa ran zai hanzarta kammala muhimman ayyukan hanyoyi a faɗin ƙasar.

David Umahi.
Ministan ayyuka, David Umahi yana magana a wurin taro Hoto: David Umahi
Source: Twitter

Ministan ya kuma bayyana cewa an kammala aikin farko na titin Abuja–Kaduna–Kano mai tsawon kilomita 118, wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 137.

Ya ƙara da cewa ana sa ran kammala ragowar kilomita 164 na aikin nan da watan Nuwamban 2026, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

FEC ta amince da gyaran NYSC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da yi wa hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) garambawul bayan shekaru 53.

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa.

A cewarsa, garambawul ɗin zai haɗa da cikakken nazari kan yadda shirin NYSC ke gudana domin ya dace da bukatun Najeriya na yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262