Matashin makiyayi ya kashe yayan sa saboda Saniya

Matashin makiyayi ya kashe yayan sa saboda Saniya

Wani matashin makiyayi, Bello Musa; mai shekaru 22, ya kashe dan uwansa saboda bacewar wata Saniya a jihar Nasarawa.

Yanzu haka matashin na tsare a sashen binciken laifuka dake ofishin hukumar 'yan sanda a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Bello ya kashe dan uwansa, Abdullahi, ta hanyar kafta masa sara da adda a wuya bayan barkewar takaddama tsakanin su a kan batan Saniya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Ahmed Bello, ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Akuwate dake karamar hukumar Doma, ranar 9 watan Maris, 2018.

Matashin makiyayi ya kashe yayan sa saboda Saniya
Matashin makiyayi

Sannan ya kara da cewar an mayar da binciken laifin sashen binciken manyan laifuka na shelkwatar jiha a ranar 25 ga watan Maris.

Da yake bayar da ba'asin abinda ya faru, Bello, ya ce ya kashe dan uwansa Abdullahi ne bayan barkewar rikici a kan wata saniya da suka tsinta kuma aka bashi ya je ya sayar da ita amma sai ta gudu.

DUBA WANNAN: Anyi wani kazamin karon batta tsakanin sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram, an rasa rayuka a kowanne bangare

Ya cigaba da cewa bayan ya sanar da dan uwan sa maganar batan saniyar sai ya ki yarda tare da yi masa barazanar zai kashe shi idan bai fito da saniyar ko kudin da ya sayar da ita ba.

Bayan sun kaure da fada ne sai ya fitar da addar sa ya kaftawa yayan nasa sara.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce zasu gurfanar da matashin gaban kotu nan bada dadewa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng