Wani Mummunan Hatsarin Mota ya salwantar da Rayuka 12 a jihar Ogun

Wani Mummunan Hatsarin Mota ya salwantar da Rayuka 12 a jihar Ogun

An tabbatar da kimanin rayuka 12 sun salwanta tare da raunatar mutane biyar a wani mummunan hatsarin motoci biyu kirar Volvo da Ford da ya afku a yankin Foursquare dake babbar hanyar Legas da Ibadan a ranar Asabar din da ta gabata.

Mista Babatunde Akinbiyi, Kakakin hukumar TRACE (Traffic Compliance and Enforcement Agency) ta kula da ka'idojin manyan hanyoyi na jihar Ogun shine ya tabbatar da afkuwar wannan tsautsayi yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai a birnin Abeokuta.

Wani Mummunan Hatsarin Mota ya salwantar da Rayuka 12 a jihar Ogun
Wani Mummunan Hatsarin Mota ya salwantar da Rayuka 12 a jihar Ogun

Akinbiyi dai ya bayyana cewa, direban mota kirar Ford shine ya janyo afkuwar tsautsayin yayin ketare wata mota dake gaban sa ta hanyar da ba ta dace ba.

A yayin da mota kirar Volvo mai zuwa ta sabanin hanya, sai kurum ba tare da aune ba suka gwabzawa juna.

KARANTA KUMA: 2019: Ka daina Yaudarar kanka - PDP ga Shugaba Buhari

Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, wannan hatsarin dai ya ritsa ne da kimanin mutane 17, inda 12 da suka hadar da mata 6 da maza 6 suka riga mu gaskiya. Sai kuma maza uku da mata biyu da kwanan su ke gaba suka raunata.

Kakakin hukumar ta TRACE ya kara da cewa, an garzaya da wadanda suka raunata zuwa asibitin Ife Oluwa dake jihar ta Ogun, yayin da aka killace gawar wadanda suka rasa rayukan su a ma'ajiyar gawawwaki ta FOS dake yankin Ipara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng