Buhari ya koka, ya ce Allah ba zai yafewa shugabannin da suka mulki Najeriya a baya ba

Buhari ya koka, ya ce Allah ba zai yafewa shugabannin da suka mulki Najeriya a baya ba

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka a kan yadda kafafen watsa labarai a Najeriya ke wallafa rahoton maganganun sa.

A wata hira da ya yi da sashen Hausa na Radiyon Amurka a birnin Washington, Buhari, ya koka a kan yadda 'yan jaridar Najeriya ke canja ma'anar kalaman sa ko kin bayyana cikakken abinda ya fada yayin jawabi ko tattaunawa da manema labarai.

Shugaba Buhari na wadannan kalamai ne dangane da batun kiran matasan Najeriya cima-zaune da ya jawo barkewar cece-kuce a Najeriya.

Buhari ya koka, ya ce Allah ba zai yafewa shugabannin da suka mulki Najeriya a baya ba
Shugaba Buhari

A yayin wata tattaunawa da shi a kasar Ingila, shugaba Buhari ya ce "kimanin kashi 60 na matasan Najeriya basa aikin komai amma suna son gwamnati tayi masu komai kyauta saboda Najeriya na da arzikin man fetur," kalaman da 'yan jarida suka ce Buhari ya kira matasan Najeriya malalata.

Kazalika shugaba Buhari ya bayyana cewar mafi yawan matasan arewacin Najeriya basu halarci makaranta ba ko kuma basu iya kammala karatu ba bayan sun fara. Saidai 'yan jarida a Najeriya sun ce ya kira matasan arewacin Najeriya jahilai.

DUBA WANNAN: Jiga-jigan jam'iyyar APC sun kauracewa yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe

Shugaba Buhari ya ce Allah ba zai kyale shugabannin Najeriya da suka cutar da jama'a ba yayin da suke kan mulki.

"Allah ne kawai zai hukunta shugabannin Najeriya da suka ki yiwa Najeriya da 'yan Najeriya abinda ya dace lokacin da suke kan mulki," in ji Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel