‘Isra’ila Ta Hallaka Dubban Yara Kanana da Gangan a Falasdinu’
- Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi Isra’ila da jawo mutuwar yara Falasdinawa a Gaza
- Rahoton ya ce hare-haren soji, katse tallafi da hana kayan agaji shiga Gaza sun haddasa mummunar illa ga rayuwa da lafiyar yara
- Isra’ila ta yi watsi da rahoton, tana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe, yayin da jami’anta suka kare matakan da suke dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wani rahoto kan zargin Isra'ila.
Rahoton yana zargin Isra’ila da ci gaba da aikata kisan kare dangi a Gaza da ke Falasdinu wanda abin takaici ne.

Source: Getty Images
Zargin Majalisar Dinkin Duniya kan Isra'ila
Rahoton da Majalisar ta wallafa a shafinta ya ce sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare da suka haddasa mutuwa, raunuka da kuma matsananciyar damuwa ga yara Falasdinawa.
A cewar kwamitin, hare-haren da ake kaiwa yara da gangan na nuna manufar lalata al’ummar Falasdinu da ke zaune a Gaza.
Shugaban kwamitin, Srinivasan Muralidhar, ya ce har bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2025 ana ci gaba da kashe yara.
Ya kara da cewa Isra’ila ta yi watsi da wajibcin kare yara Falasdinawa kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Sai dai gwamnatin Isra’ila ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa rahoton wani yunkuri ne na yada farfaganda a kanta.

Source: Getty Images
Martanin da Isra'ila ta yi kan zargin
Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya, Danny Danon, ya soki rahoton tare da kare matakin kasarsa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa katse kayan agaji da magunguna ya kara jefa yara cikin mawuyacin hali a Gaza.
An ce hare-hare kan asibitoci da cibiyoyin lafiya sun haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki da kwakwalwar yara.
Rahoton ya bayyana cewa duk da tsagaita wuta, hare-haren sama na ci gaba da hallaka Falasdinawa da dama a Gaza.
An kuma zargi Isra’ila da fadada ikon sojinta a wasu yankunan Gaza tare da takaita zirga-zirgar mazauna yankin.
A Yankin Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Kudus, rahoton ya ce an samu karuwar tashe-tashen hankula kan yara Falasdinawa.
Kwamitin ya zargi sojojin Isra’ila da amfani da karfi fiye da kima wajen tsoratarwa da kuma ladabtar da yara.
Rahoton ya ce an kuma kama yara da dama ba tare da bin ka’idojin doka ba, yayin da wasu ba a san inda suke ba.
Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta yaba da rahoton, tana mai cewa ya sake bayyana gazawar duniya wajen dakatar da cin zarafi.
Kwamitin ya bukaci Isra’ila ta dakatar da ayyukan soji a Gaza tare da mutunta hakkokin yara kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Iran: Isra'ila ta so taimaka wa masu zanga-zanga
A wani labarin, an ji cewa tsohon Firaministan Isra’ila, Naftali Bennett, ya bayyana yadda kasar ta shigar da na’urorin Starlink a boye zuwa Iran.
Bennett ya bayyana cewa an shirya samar da dubban na’urori domin tabbatar da ci gaba da intanet da kafafen sada zumunta a Iran.
Ya zargi gwamnatin Benjamin Netanyahu da dakatar da shirin, lamarin da ya hana masu zanga-zanga cin gajiyar tsarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

