Peter Obi da Kwankwaso Sun Tashi Tsaye sai Sun Hana Soke Rajistar Jam'iyyar NDC
- Hukuncin alkalin kotun tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ya tada hankalin shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC a Najeriya
- Kotu ta canza matakin da ta dauka, ta yi umarni a soke rajistar da aka yi NDC ‘yan kwanaki bayan jam’iyyar ADC ta fuskanci barazana
- Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da za su yi takara a jam’iyyar hammayar sun shiga yin zama da nufin su daukaka kara a kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugabannin jam’iyyar NDC sun dage da zama dare da rana domin ganin sun yi nasarar tsaida ‘yan takara a zabe mai zuwa da za a yi.
Hakan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotun tarayya mai zama a garin Lokoja, jihar Kogi ta rusa rajistar da aka yi wa jam’iyyar NDC.

Source: Twitter
Hukuncin kotu ya sa shugabannin NDC taron gaggawa
Hukuncin da aka yanke a ranar Juma’a ya sa jagororin jam’iyyar hamayya sun hada kai domin ganin sun shiga takara a cewar jaridar Punch.
Wani babba a jam’iyyar NDC ya shaida cewa ana ta yin zaman gaggawa domin ganin an tunkari matsalar soke rajistar a kotun daukaka kara.
Jami’in da ya yi magana ba tare da ya bari an kama sunan shi ba, ya tabbatar da cewa NDC tana duba dabarar da za ta iya amfani da shi a kotu yau.
A sakamakon haka ne Peter Obi, Seriake Dickson da shugaban jam’iyya da sakatarensa na kasa da wasu many ana NDC suka zauna a ranar Lahadi.
“An yi wasu zama a bayan labule tun bayan fitowar hukuncin kotun tarayya na Kogi.
Alal Misali, Obi, Sanata Dickson, shugaban jam’iyya na kasa, sakatare da wasu shugabanni sun halarci taron gaggawa da aka yi jiya.
- Wani babba a NDC
Jam'iyyar NDC za ta je kotun daukaka kara
Ko a lokacin da yake magana, ya tabbatar da cewa akwai shirye-shirye da ake yi na yin wani zaman gaggawa domin a daukaka kara yau a gaban kotu.
Zuwa yanzu bai san lauyoyin da za su jagoranci shigar da karar ba, amma ya sa san Reuben Egwuaba ne kan gaba wajen zuwa babban kotu.
Reuben Egwuaba shi ne mai ba jam’iyyar NDC shawara a kan harkokin shari’a a matakin kasa.

Source: Twitter
Sakataren NDC a Najeriya, Ikenna Enekweizu ya iya tabbatar wa duniya cewa ranar Litinin ne lauyoyin jam’iyyar za su daukaka kara a kotu.
Amma shi ma Enekweizu bai fadi lauyoyin da za su tsaya wa jam’iyyar ta NDC ba. A maganganunsa, ya yi kaca-kaca da hukuncin da alkali ya yi.
Rabiu Kwankwaso ya zauna da Dickson
Bayan duk zaman da aka yi a baya, sai aka ji Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da jagoran NDC na kasa wato Seriake Dickson a birnin Abuja.
Madugun Kwankwasiyya ya ziyarci tsohon gwamnan ne har gida domin ganin yadda za a bullo wa lamarin, ya bayyana haka jiya a dandalin X.
Sanata Kwankwaso ya an yi zaman ne a kokarin ganin NDC ta shirya wa babban zabe na 2027.
‘Dan takarar na mataimakin shugaban kasa ya kira abin da ya faru da jam’iyyar NDC a matsayin wani karamin cikas da za a samu a shawo kan shi.

Kara karanta wannan
"Ba yan bindiga ba ne," Rundunar 'yan sanda ta fadi wadanda aka gani dauke da bindigu a bidiyo
Obi da Kwankwaso sun koma NDC
A farkon watan Mayu aka rahoto cewa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana komawarsu jam’iyyar NDC a hukumance, bayan fice wa daga ADC.
'Yan siyasar sun yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji yawan shari’o’in kotu, su mayar da hankali kan ci gaban ƙasa da kuma haɗin kan al’ummar Najeriya.
A bikin shigarsu NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun aika muhimmin sako ga magoya bayansu yayin ake tunkarar babban zabe a farkon shekarar 2027
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

