An gano mai kista duk wani makirci na hare-haren jihar Benuwe

An gano mai kista duk wani makirci na hare-haren jihar Benuwe

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yi nasarar cafke wani dan Boko Haram da ake zargi da kitsa makirci wajen shirya mafi akasarin hare-haren da suka afku a jihar Benuwe a kwana-kwanan nan.

Wannan shu'umin mutum mai sunan Aminu Yaminu ya shiga hannun hukuma wanda ya fi shahara da sunan Tashaku.

Majiyar rahoton dai ta bayyana cewa Tashaku ya shiga hannun sakamakon hadin gwiwar dakarun soji, jami'an 'yan sanda da kuma na hukumar DSS, inda suka damke a babban birnin Makurdi na jihar ta Benuwe.

Aminu Yaminu (Tashaku)
Aminu Yaminu (Tashaku)

Hukumar Sojin ta bayyana cewa ta na da yakinin Tashaku shine ummul aba isin mafi akasarin hare-hare na kwana-kwanan nan da suka afku a jihar Benuwe.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta bayar da tabbacin zartar da wasu sabbin dokoki 2 a harkar Lafiya kafin 2019

A sakamakon bincike na leken asirin da hukumomin tsaron suka gudanar, tuni dai wannan mamugunci ya kammala shirye-shiryen sa da 'yan ƙungiyar sa dake jihohin Bauchi, Borno, Yobe da kuma Nasarawa akan zartar da wannan mummunan hari mai girman gaske a jihar Benuwe.

Hukumomin tsaro sun sha alwashi na tabbatar da masu gaba da zaman lafiya a jihar sun shiga hannu, yayin da suke shawartar al'ummar jihar akan ci gaba da gudanar da al'amurran su ba tare da wata fargaba ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel