Wani Yaro ya rataye kansa bayan Mahaifin sa ya ƙi saya masa Mota

Wani Yaro ya rataye kansa bayan Mahaifin sa ya ƙi saya masa Mota

Wani ibtila'i mai ban tausayi ya afkawa wani dangi a kasar Uganda, yayin da wani matashin yaro ya yiwa kansa kisan gilla sakamakon mahaifin sa da ya ƙi saya masa Motar hawa ta kansa.

Wannan matashin yaro mai sunan Kawa, ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a unguwar Kagando ta garin Kisinga dake kasar Uganda.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, mahaifin yaron, Mugenyi, ya hau kujerar na ƙi ta sayawa dan sa Mota bayan da ya jima yana masa magiya domin marari na cikar burin sa.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wannan matashi ya sha yunkurin kashe kansa da diddikar guba har a karo uku inda ake takar sa'a 'yan uwan sa ke hana shi.

KARANTA KUMA: A dakatar da Kashe-Kashen jihar Benuwe - Shugaban jam'iyyar PDP ya yi kira ga shugaba Buhari

An tsinto gawar Kawa ne rataye a ranar 24 ga watan Afrilu a gidan su wanda ya dade yana fafutikar kashe kansa ta kowane hali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel