Kauracewa Kwanciyar Iyali: Wata Mata ta roki Kotu ta raba auren ta da Mijin ta

Kauracewa Kwanciyar Iyali: Wata Mata ta roki Kotu ta raba auren ta da Mijin ta

Wata matar aure Sandra Ekpa, ta roki babbar kotun garin Mararaba a jihar Nasarawa akan ta raba tsohon auren ta da ta yi shekaru uku da suka gabata a sanadiyar mai gidan ta da ya kauracewa kwanciya da ita gami da aikata tsubbace-tsubbace.

Sandra a ranar Juma'a ta yau ta shaidawa kotun cewa, mijin ta Giseon Adejoh, ya gurbata rayuwar auren su tare da kashe soyayyar da a baya can take yi a gare shi.

Wannan mata dai ta bayyana cewa, sun yi auren su na soyayya tun a ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 2015 a bisa al'adar su ta gargajiya ta kabilar Igala a jihar Kogi inda suka azurta da da daya tilo tun gabanin nan.

Kauracewa Kwanciyar Iyali: Wata Mata ta roki Kotu ta raba auren ta da Mijin ta
Kauracewa Kwanciyar Iyali: Wata Mata ta roki Kotu ta raba auren ta da Mijin ta
Asali: UGC

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wannan mata ta bayyana cewa tun bayan haihuwar ta mijin ya kauracewa kwanciya da ita wanda a yanzu watanni 18 kenan kuma ya kama tsubbace-tsubbace domin neman duniya.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mata dai ta yi iyaka bakin kokarin ta don ganin sun gyara zamantakewar su ta aure amma lamarin ya ci tira da a yanzu ta yanke hukunci sawwakewa mijin ta.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta bankado wani makamakin kare Dangi da muggan Bindigu 13 a jihar Kebbi

A yayin haka kuma Sandra tana rokon kotu akan umartar mijin na ta da biyan N30, 000 a kowane wata da zai taimaka ma ta wajen ci gaba da dawainiya da yaron da suka haifa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Adejoh ya karyata wannan tuhuma da uwargidan sa ke yi inda ya roki kotun da ta bashi lokaci na samun damar sansantawa da mai dakin sa wajen mayar da komai ba komai ba.

Alkalin Kotun Mista Ibrahim Shekarau, ya daga sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Mayu domin jin ta bakin kowane daga cikin su dangane da hukuncin da suka yanke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel