Hotunan wasu rikakkun barayi dake kwacen motocin alfarma
Jami'an yan sanda sun kama wasu kwararrun barayi dake kwacen motocin alfarma da suka addabi jihar Anambra da kewaye.
A jiya Laraba ne kwamishinan yan sanda, malam Garba Umar, ya yi bajakolin barayin ga manema labarai a shelkwatar yan sanda dake jihar.
Umar ya ce, jami'ansu sun kuma gano wasu manyan-manyan motoci 11 da aka yi fashin su a gurare daban-daban a hannun wadanda ake zargin.
Cikin motocin da aka samu nasarar kwatowa hannun barayin sun hada da Lexus, Mercedes Benz, Toyota da sauransu.
Kwamishinan ya ce rundunar su ta rubanya kokarinta don tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama'a.
DUBA WANNAN: Buhari ya koka, ya ce Allah ba zai yafewa shugabannin da suka mulki Najeriya a baya ba
Wadanda ake zargin sun hada da Johnson Aerfa, Chibueze Ebenyi daga kauyen Ushon jihar Ondo wanda ake zargin shi yake horon gunguj barayin, da kuma Chibuike Ugwu.
Malam Umar ya ce, wadanda ake zargin za'a gabatar da su gaban kuliya don yi masu shari'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng