Bautar bishiya a Kano: An raunata 'yan Hisbah a rikicin sare ta

Bautar bishiya a Kano: An raunata 'yan Hisbah a rikicin sare ta

Gano wata bishiya mai hoton ka'aba a karamar hukumar Kunci dake jihar Kano ya zo da rudani da kuma babban kalubale.

Da farko batun bishiyar ya zama abin al'ajabi, inda jama'a ke tururuwar zuwa ganin ta kafin daga bisani jama'a su fara zuwa gaban bishiyar domin yin addu'o'i.

Ganin karbuwar da bishiyar ta samu ne sai wasu matasa suka kewaye bishiyar tare da karbar kudi ga duk mai son ganin bishiyar domin neman tabarraki ko yin dawafi.

Bautar bishiya a Kano: An raunata 'yan Hisbah a rikicin sare ta
Bishiyar da ake bauta a Kano bayan an sare ta

Bayan labari ya isa hukumar Hisbah ne sai ta tura jami'an ta domin su sare bishiyar saboda barazana da illar da take da ita ga imanin musulmi.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Bam ya fashe a garin shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo

Sai dai an yi dauki ba dadi da matasan dake karbar kudi a wurin bishiyar da jami'an Hisbah har ta kai ga sun sassari 'yan Hisbah tare da karya wasu.

Matasan da suka yi wannan aika-aika sun cika wandon su da iska yayin da jami'an Hisbah ke samun kulawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng