Fusatattun 'yan Achaba sun lakadawa wani VIO na jaki Abuja, karanta dalili

Fusatattun 'yan Achaba sun lakadawa wani VIO na jaki Abuja, karanta dalili

Wasu fusatattun 'yan Achaba sun lakadawa wani jami'in binciken ababen hawa (VIO) duka a Abuja.

Kakakin jami'an VIO a Abuja, Mista Kalu Emetu, ya sanar da haka ga kamfanin dillancin labarai (NAN) yau a Abuja tare da bayyana sunan jami'in da aka da Mista Abubakar Eyge.

Ya bayyana lamarin ya faru ne jiya, Litinin, a shataletalen Area 1 dake yankin Garki.

Fusatattun 'yan Achaba sun sun lakadawa wani VIO na jaki Abuja, karanta dalili
Fusatattun 'yan Achaba sun sun lakadawa wani VIO na jaki Abuja

A cewar sa, 'yan Achabar sun yiwa VIO din rajamu ne a yayin da yake kokarin saka wani da jami'an suka kama zuwa babban ofishin su dake Wuse.

Kakakin ya ce 'yan Achabar sun yi dandazo tare rufe jami'in da duka har ta kai ga sun yi masa rauni.

DUBA WANNAN: 'Yan sandan Najeriya sun dakile wani mummunan harin kunar bakin wake a jihar Borno

Ya kara da cewar lamarin kan iya fin haka tsamari ba don jama'a dake wucewa sun kwaci VIO din ba.

Yanzu haka an kai Mista Eyge asibiti domin duba lafiyar sa a yayin da aka shigar da korafi ofishin 'yan sanda.

Kakakin ya ce hari kan jami'an VIO na kara yawaita a garin Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng