Sojoji Sun Bindige 'Yan Bindiga da Suka Nufi Kasuwa kai Hari
- Dakarun Najeriya karkashin Operation Whirl Stroke tare da 'yan sa-kai sun dakile wani hari da ake zargin 'yan ta'adda sun shirya kai wa a kasuwa a Benue
- Yayin da aka fafata, sojojin sun kashe mutane biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne tare da ƙwato makamai da wasu abubuwa da dama
- Rundunar ta yaba wa sojojin da jami'an tsaron jihar, tare da kira ga jama'a su ci gaba da ba hukumomi bayanan da za su taimaka masu wajen samun nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Dakarun Operation Whirl Stroke tare da haɗin gwiwar 'yan sa-kai sun dakile wani hari da ake zargin 'yan ta'adda ne suka shirya shi a Benue.
Sojojin sun kashe mutane biyu da ake zargi 'yan bindiga ne tare da ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka gudanar.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa sojojin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin jami'in yaɗa labaran su, Laftanar Ahmad Zubairu, ya fitar a ranar Lahadi.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga
A cewar sanarwar, an gudanar da samamen ne bayan samun kiran neman agaji yayin da sojojin ke sintiri domin yaƙi da kuma ƙarfafa amincewar jama'a a yankin kasuwar doya ta Tor Donga da ke jihar.
“Da isarsu wurin, sojojin sun yi arangama da 'yan ta'addan tare da fafatawa da su.
"A yayin artabun, an kashe mutane biyu da ake zargin 'yan ta'adda ne, waɗanda aka bayyana sunayensu da Dantaraba da Golozo,”
In ji wani ɓangare na sanarwar.

Source: Original
Kayayyakin da sojoji suka kwato
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, jakar harsashin AK-47 guda ɗaya, bindiga ƙirar pistol da ta lalace guda ɗaya, jakar harsashin pistol guda ɗaya, harsasai shida na NATO.

Kara karanta wannan
Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu
Haka zalika sun kwato harsasai tara na bindigar pistol mai girman 9mm, katin ATM guda ɗaya, katin ATM na Moniepoint guda ɗaya da wasu kayayyaki daban-daban.
An yaba wa sojojin Najeriya
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Whirld Stroke, Manjo Janar Moses Gara, ya yabawa sojojin kan ƙwarewa, jajircewa da kuma saurin ɗaukar mataki da suka yi.
Ya yi magana yana mai cewa hakan ya hana aukuwar mummunar asarar rayukan fararen hula da kuma tangarɗar harkokin tattalin arziki.
Premium Times ta rahoto cewa ya kuma yabawa jami'an sa-kai na jihar Benue bisa haɗin gwiwar da suke yi da sojoji wajen yaƙi da aikata laifuffuka a faɗin jihar.
Gara ya gode wa jama'a kan ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci, tare da roƙon mazauna yankin su ci gaba da ba su haɗin kai.
An kashe shugaban Fulani
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mutane dauke da makamai sun kashe shugaban Miyetti Allah na jihar Benue, Ardo Risku.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shugaban ne yayin da yake komawa gida daga wani taron zaman lafiya da aka yi a jihar.
Kashe Ardo Risku ya dauki hankalin jama'a da kungiyoyi a Najeriya, inda gwamnatin Benue ta ce za ta tabbatar da an dauki mataki.
Asali: Legit.ng
