Sanatan da ya fara kiran tsige Buhari ya sha rankwashi wurin wani matashi

Sanatan da ya fara kiran tsige Buhari ya sha rankwashi wurin wani matashi

Sanata mai wakiltar jihar Edo ta kudu, Matthew Urhoghide, ya bayyana abinda ya faru da shi bayan gabatar da kudirin tsige Buhari a zauren majalisa.

Sanata Urhoghide ya ce baya nadamar gabatar da kudirin tsige Buhari tare da bayyana cewar shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Edo, Taiwo Akerele, ne ya turo matasan da suka ci masa mutunci a filin tashi da saukar jirage ranar Juma'a.

Da yake bayyana abinda ya faru gare shi, Urhoghide, ya ce "dama na san sun shirya ci min mutunci tun kafin na bar Abuja. Bayan na sauka sai kwamishinan 'yan sanda ya bani shawarar na jira gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki kuma nayi biyayya da shawarar hakan.

Sanatan da ya fara kiran tsige Buhari ya sha rankwashi wurin wani matashi
Sanatan da ya fara kiran tsige Buhari ya sha rankwashi wurin wani matashi

Bayan gwamnan ya zo muna tafiya tare muna hira kafin karasawa inda motocin mu ke jira sai kawai wani yaro ya rankwashi kai na amma gwamna ko tsayawa bai yi ba, sai kawai ya cigaba da tafiya."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan sara-suka sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Kaduna, sun raunata wasu

Urhoghide ya kara da cewar ba kankanin cin mutunci bane a ce karamin yaro zai bugi Sanatan Najeriya, wakilin jama'a.

Urhoghide ya ce babu abinda zai hana shi gudanar da aikin sa na majalisa tare da bayyana cewar zai nemi hakkin sa a kotu, ta hanyar gurfanar da duk masu hannu cikin shirya masa wannan cin mutunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel