Abun Al Ajabi
Masu hikimar zance sun ce mata da kudi sai Allah! Hakan ce ta kasance ga wata amarya inda ta zage tana kwasar dalolin da ake lika mata a wajen liyafar bikinta.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) a shekarar 2020 a kididdigar kiwon lafiya ta duniya ta nuna cewa adadin rayuwar 'yan Najeriya ya kan kai 62.6 har zuwa mutuwarsu.
Wani bidiyo da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana koyawa jikansa yadda ake gaishe da manya da suka girma
Kauyukan Gidna da Gidan-Dogo da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna sun magantu a kan yadda yan bindiga suka farmaki masu zaman makoki da sace mutane.
Wani direban adaidaita sahu ya shiga hannu bayan ya kasa biyan kudi har naira miliyan 3.7 daya ranta sannan ya salwantar da su a gidan rawa ta hanyar liki.
David Sakayo Kaluhana mai mata 15 da yara 107 ya bayyana cewa tsantsar wayo irin nasa ne ya sanya shi tara iyali da yawa don mace daya ba za ta iya da shi ba.
An haife shi kuma ya girma a garin Karofi na karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina, Yazid mai digirin digir daga BUK yanzu ya koma sana'ar jari bola a Legas.
Wani matashi 'dan Najeriya mai suna Alhasssan Ibrahim, 'dan asalin jihar Kano dake siyar da tsire a Ibadan, ya samuu sauyin rayuwa baki daya a lokaci daya.
Wata mata mai matsakaicin shekaru ta sauya tunanin mallam Bahaushe na son ganin mace ta zauna a gida ba aiki. Matar dai ta kama sana’ar tuka adaidaita sahu.
Abun Al Ajabi
Samu kari