Kada Ka Gwada A Najeriya: Akwatin Kaya Na Bature Yana Biye Da Shi Yayin Da Yake Tafe
- Wani Bature ya haddasa cece-kuce bayan an gano shi a wani filin jirgin sama yana tafiya tare da akwatin kayansa wanda ke tuka kansa
- A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano akwatin kayan na tafiya da kansa kuma hakan ya baiwa mutanen da suka kalli bidiyon a TikTok mamaki
- Sai dai kuma, hakan bai burge wasu ba inda suka ce za a iya sace jakan va tare da sanin mai shi ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
An hasko wani bature a bidiyo yana baje kolin akwatin tafiyarsa wanda ke tuka kansa da kansa.
A cikin bidiyon wanda ya yadu, an gano shi yana tafiya a wani filin jirgin sama yayin da akwatin kayan nasa ke biye da shi a baya.
Babu wanda ke tura akwatin. Shi da kansa yake tuka kansa kuma hakan ya baiwa mutane da dama da suka ga bidiyon mamaki.

Kara karanta wannan
Soyayya Ruwan Zuma Dadi: Bidiyon Bature da Masoyiyarsa Bakar Fata Sune Holewa A Bakin Hanya

Asali: UGC
Koda dai abun ya kayatar sosai kuma ya saukaka wahala, mutane da dama sun soki akwatin sannan sun lissafa aibun shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata matashiya mai suna @chuka_jim a TikTok ta bayyana cewa ana iya sace akwatin ba tare da mai shi ya sani ba tunda kawai tafiya yake a bayansa.
Masu amfani da TikTok sun bayyana ra’ayoyinsu
@onecooljk ya ce:
“Kawai..sai batirin yak are..kuma sai gane cewa ya rasa jakarsa kimanin mintuna 30 suka shiga.”
@itsjustastory ya rubuta:
"Wasu jiragen ba za su yarda da su a jirgin ba don haka ku lura idan kun mallaki daya."
@crazypugguy ya ce:
"Diyata na amfani da keken guragu kuma wannan zai taimaka sosai wajen tafiya ba tare."
@amanwithdreams ta yi martani:
"Na tabbata ba za ka iya yin hakan a kasata ba. Za su sace shi cikin sakonni kada."
@redflower096 ta ce:
"Yana da kyau a irin wadannan kasashen amma wasu kasashen za ka juya ka nemi akwaitin ka rasa."
Kalli bidiyon a kasa:
“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai
A wani labarin, wani dan Najeriya mazaunin Ingila ya je shafin soshiyal midiya don nuna wani bidiyonsa yana tafiya shi kadai a titi.
Mutumin wanda ke alfahari da kansa ya ce titunan sun zama wayam ne saboda duk Turawa sun gudu saboda tsoron zafin rana.
Da yake magana a cikin harshen Igbo, mutumin wanda ke amfani da shafin TikTok ya ce shawarar da gwamnatin Ingila ta baiwa al’ummar kasar shine ya sa unguwanni da tituna suka yi wayam.
Asali: Legit.ng