Kwana Ya Kare: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Farfesa Gregory Ikechukwu Ibe, wanda ya kafa Jami’ar Gregory da ke Uturu a jihar Abia, ya rasu yana da shekara 63
  • Ibe, wanda ya tsaya takarar gwamnan Abia a ƙarƙashin jam’iyyar APGA a zaɓen 2023, ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya
  • Iyalnsa sun ce za a tuna da shi bisa gudummawar da ya bayar a fannin ilimi, kasuwanci da ci gaban al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Wanda ya kafa kuma mamallakin Jami’ar Gregory da ke Uturu, jihar Abia, Farfesa Gregory Ikechukwu Ibe, ya rasu.

Ibe, wanda ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar Abia a ƙarƙashin jam’iyyar APGA a zaɓen 2023, ya rasu ne a ranar Lahadi yana da shekara 63 bayan fama da doguwar jinya, a cewar iyalansa.

Kara karanta wannan

Lokacin tafiya ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya ya rasu yana da shekaru 71 a duniya

Gregory Ikechukwu Ibe
Farfesa Gregory Ikechukwu Ibe, wanda ya yi takarar gwamnan jihar Abia a zaben 2023 karkashin inuwar APGA Hoto: Cosmas Ozigbo
Source: Twitter

Iyalan gidan sarauta na Mai Martaba Eze Cyril Ibe, Okwelube na Farko ne suka sanar da rasuwarsa a ranar Litinin cikin wata sanarwa, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Gudummuwar Farfesa Ibe

An bayyana marigayin a matsayin fitaccen malamin jami’a, shugaba, mai taimakon jama’a, ɗan kasuwa kuma masani a fannin ilimi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen faɗaɗa damar samun ilimi, da taimaka wa marasa galihu.

Sanarwar ta ce:

“Ta hanyar Jami’ar Gregory da ke Uturu, kamfanin Skill ‘G’ Ltd., Innov8 Hub da sauran shirye-shiryensa, ya sauya rayuwar dubban mutane, tare da barin gado mai ɗorewa a fannin ilimi da ci gaban al’umma.”

Farfesa Ibe ya mutu ya bar ’ya’ya shida da jikoki bakwai. Iyalansa sun nuna godiya bisa addu’o’i da saƙonnin ta’aziyya da suka samu tun bayan rasuwarsa.

Sun kuma kara da roƙon jama’a su ci gaba da yi masa addu’ar Allah Ya jiƙansa, Ya kuma ba wa iyalansa haƙurin jure wannan rashi.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa 8 da suka bar APC sun canza shawara bayan haɗuwa da Shugaba Tinubu

Sun ce za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba, sannan suka buƙaci jama’a su mutunta sirrinsu a lokacin makoki.

Yadda ya nemi mulkin Abia a 2023

Marigayin, wanda farfesa ne a fannin nazarin harkokin kasuwanci, ya yi kira da a sauya ikon mulkin jihar Abia zuwa yankin Abia ta Arewa a zaɓen gwamna na 2023, bisa la’akari da yarjejeniyar karba karba ta jihar, wato Abia Charter of Equity.

Punch ta ruwaito cewa ya fara fuskantar matsalolin lafiya ne a lokacin da harkokin siyasa suka fara ƙamari gabanin zaɓen 2023. Tun bayan zaɓen, ba kasafai yake fitowa fili ba yayin da yake fama da rashin lafiyar.

Gregory Ibe
Wanda ya kafa jami'ar Gregory, Farfesa Gregory Ibe Hoto: Cosmas Ozigbo
Source: Twitter

Sai dai ya halarci jana’izar mahaifiyarsa a farkon wannan shekara.

Ibe, fitaccen ɗan kasuwa kuma mai zuba jari ɗan ƙabilar Igbo, ya kuma shahara wajen taimakon jama’a, musamman tallafa wa ɗaliban jami’a da ke karatu a Jami’ar Gregory bisa tallafin karatu.

Tsohon gwamnan Delta ya rasu

Kun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Delta, Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 71 da haihuwa a duniya.

Iyalan marigayin sun bayyana rasuwar Uduaghan a matsayin babban rashi ga iyalansa, Jihar Delta da Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262