Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

  • Wani dan Najeriya ya wayi gari cikin tashin hankali bayan ya gano hotunansa a TikTok dauke da rubutun 'Allah ya ji kanka'
  • Wata 'yar TikTok ce ta tsara bidiyo da hotunan Chima sannan ta wallafa a shafinta a matsayin kawunta da ya mutu kwanaki
  • Da yake Allah wadai tare da nuna takaicinsa a kan lamarin, matashin ya jaddada cewa yana nan da ransa bai mutu ba

Wani matashin dan Najeriya mai suna Chima ya cika da mamaki bayan ya gano cewa wata ‘yar TikTok ta yi amfani da hotunansa a shafinta, inda ta yi ikirarin cewa shi din kawunta ne da ya mutu kwanan nan.

‘Yar TikTok din ta yi amfani da hotunan Chima wajen tsara wani bidiyo dauke da rubutun da ke nuna cewa shi din ya mutu.

Kara karanta wannan

Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka

Chima
Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta Hoto: LIB
Asali: UGC

Matashin ya je shafinsa na Twitter domin nuna takaicinsa a kan wannan abu da ‘yar TikTok din ta yi masa.

Ya rubuta a shafin nasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Na wayi gari da safiyar nan kawai sai na tsinci cewa wata ta yi bidiyo a TikTok da hotuna na. cewa ni din marigayin kawunta ne da aka binne a ranar 6 ga wannan watan. Magana ta gaskiya ban san ya zan ji ba. wani irin mugun wasa ne wannan. Ban san wacece ita ba kuma magana ta gaskiya ban mutu ba.”

kalli wallafar tasa a kasa:

Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka

A wani labarin, Dharamdev Ram, ya kasance tsoho mai shekaru 62 daga yankin Bihar a kasar Indiya kuma ya shafe tsawon shekaru 22 ba tare da ya yi wanka ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Al’ummar kasar Indiya sun yi martani bayan samun wannan labari na rashin wankan Ram, Aminya ta nakalto.

Ram dai ya yi suna sosai a kauyensa na Baikunthpur, inda kowa ya san cewa baya sanyawa kowani bangare na jikinsa ruwa tsawon shekaru 22.

Asali: Legit.ng

Online view pixel