Sanata Tambuwal na Shirin Ficewa daga ADC zuwa APC? An Ji Yadda Zancen Yake
- Ofishin Aminu Tambuwal ya bayyana rahotannin cewa yana shirin komawa APC a matsayin ƙarya marar tushe
- Mai ba sanatan shawara kan yaɗa labarai, Prince Daniel, ya ce hulɗar Tambuwal da ’yan siyasa daga wasu jam’iyyu ba ta nuna shirin sauya sheƙa ba
- Ofishin ya jaddada cewa Tambuwal na ci gaba da kasancewa cikin ADC, inda yake ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar da tattara goyon baya gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Ofishin yaɗa labaran tsohon gwamnan Jihar Sokoto kuma sanata, Aminu Tambuwal, ya musanta rahotannin da ke cewa jigon n jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ofishin ya bayyana zargin a matsayin ƙarya marar tushe, yana mai cewa Tambuwal na nan daram a ADC kuma ya mayar da hankali wajen ƙarfafa jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Ofishin Tambuwal ya musanta shirin komawa APC
Jaridar The Punch ta ce a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026, mai ba sanatan shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Prince Daniel, ya ce babu wani shiri da Tambuwal ke yi na komawa APC.
Ya buƙaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta game da yiwuwar sauya sheƙar tsohon gwamnan.
Wani bangare na sanarwar ya ce:
“Domin kawar da duk wani shakku, Sanata Tambuwal ba shi da shirin shiga APC. Zarge-zargen da ke nuna akasin haka ƙarya ne, ba su da tushe, kuma ya kamata a yi watsi da su.”
Hotuna da bidiyo sun jawo jita-jitar sauya sheƙa
Musanta shirin ya zo ne bayan wasu hotuna da bidiyoyi sun yaɗu a kafafen sada zumunta, lamarin da ake ganin ya ƙara rura jita-jitar cewa Tambuwal na shirin sauya sheƙar siyasa.
Sai dai ofishinsa ya ce hulɗarsa da ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban bai kamata a ɗauke ta a matsayin alamar cewa yana shirin barin ADC ba.
Daniel ya bayyana cewa girmama juna a siyasa ba hujja ba ce ta sauya sheƙa.
“Mu’amala cikin mutunci a siyasa ba hujja ba ce ta sauya sheƙa. Gaisawa ko yin hulɗa da ’yan wata jam’iyya ba yana nufin ana tattaunawa kan sauya mubaya’a ba.” In ji shi.
Tambuwal na nan a ADC gabanin zaɓen 2027
Sanarwar ta bayyana Tambuwal a matsayin gogaggen ɗan siyasa da ke da kyakkyawar alaƙa da mutane daga ɓangarorin siyasa daban-daban.
Ta ƙara da cewa an gina waɗannan alaƙoƙi ne tsawon shekaru ta hanyar hidimar jama’a da mutunta juna.
Ofishin ya jaddada cewa Tambuwal bai sauya matsayinsa na siyasa ba, kuma har yanzu yana tare da ADC.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Sanata Tambuwal na nan daram a ADC. Hankalinsa ya karkata ne wajen ƙarfafa jam’iyyar, gina haɗin kai mai faɗi da tattara goyon bayan ’yan Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.”

Source: Twitter
Tambuwal ya kai karar gwamnatin Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Aminu Tambuwal, ya kai gwamnatin jihar ƙara a babbar kotun jihar bisa zargin hana shi samun rahoton kwamitin binciken shari’a da ya binciki gwamnatinsa.
Sanata Tambuwal yana neman kotu ta tilasta wa gwamnati sakin cikakken rahoton kwamitin da gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ta kafa domin binciken ayyukansa da harkokin kuɗi da sauran al’amuran gwamnatinsa na shekaru takwas.
Asali: Legit.ng


