Bidiyon Budurwa Tana Koyawa Yan Mata Dabaru kan Yadda Za Su Tambayi Iyayensu Maza Kudi

Bidiyon Budurwa Tana Koyawa Yan Mata Dabaru kan Yadda Za Su Tambayi Iyayensu Maza Kudi

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta nunawa yan mata dabarun da za dunga yi kafin su je tambayar kudi a wajen iyayensu maza
  • Budurwar ta bayyana cewa yana da kyau mutum ya je babu kwalliya, ya sanya doguwar riga sannan ya dauki littafi mai tsarki kafin ya tunkare sa
  • Mutane da dama wadanda suka yi martani ga bidiyon sun bayyana yadda suke kwashewa da iyayensu maza da kuma yadda suke amsa bukatunsu a gida

Najeriya - Wata matashiyar budurwa ta shirya bidiyo mai ban dariya tare da mahaifinta yayin da take koyawa yan mata hanya mafi dacewa da Za su bi don karbar kudade daga iyayensu maza.

Ta bayyana cewa abu na farko shine kada mace ya yarda ta sanya gashin doki mai kala. Maimakon haka ta saka gashi baki mara kyan gani.

Kara karanta wannan

Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya

Budurwa da babanta
Bidiyon Budurwa Tana Koyawa Yan Mata Dabaru kan Yadda Za Su Tambayi Iyayensu Maza Kudi Hoto: TikTok/@bhee_chee
Asali: UGC

Bayan nan, ta goge kwalliyar fuskarta sannan ta bar fuskar fayau. Budurwar ta ce bayan nan, abu na gaba shine saka doguwar riga.

Sannan kafin ta tunkari mahaifin nata, sai budurwar ta dauki wata jaka ta saka littafi mai tsarki a ciki kamar mai zuwa wajen bauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ta tambayi mahaifin nata kudi N5000, sai mutumin ya yi turus kafin ya bata wasu kudade a cikin bidiyon barkwancin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Fauzah Babadia ta ce:

"Mataki na farko: ya zamana kana da mahaifi."

janetmichael856 ta ce:

"kin yi sa'a, Allah ya albarkace shi sannan ya bar maki shi."

Missparkers ta ce:

"Mahaifina ba zai amsaba sai tuna maki cewa yana gida mana gida."

Precious ta ce:

"Mahaifina zai tambaye ni me yasa nayi shiga kamar mara galihu."

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya

A wani labarin kuma, gaskiya ne maganar cewa yara na kallon manya wajen fahimtar abubuwan da ke kewaye da su a duniya.

Hakan ne yasa suke bi duk wani sahu nasu. A wani bidiyo da ya yadu a shafin TikTok, an gano wata karamar yarinya tana jerawa kakanta inda ta dunga kwaikwayon duk wani motsi nasa.

Harma ta sanya hannayenta a bayanta sannan ta dunga tafiya kamar yadda tsohon ke tafiya. Abun ya baiwa mutane dariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel