Bidiyo: An Kama Mata Ta Saci Zinarin N1.5m a Wani Shago da Salo Mai Bada Mamaki

Bidiyo: An Kama Mata Ta Saci Zinarin N1.5m a Wani Shago da Salo Mai Bada Mamaki

  • Wata mata ta bai wa jama'a mamaki yayin da ta shiga wani shagon siyar da zinari tare da sace zinari har na N1.5 miliyan
  • A bidiyon da aka fitar ta TikTok, an bayyana cewa matar ta hadiye zinarin ne domin ta samu saukin ficewa sa shi daga shagon amma aka kama ta
  • An ji matar tana rokon mai nadar bidiyonta da ya taimaka mata kada ya saka a Facebook, shima yana da 'ya'ya kamar yadda take da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bidiyon wata mata tana sata ya matukar bai wa jama'a mamaki saboda irin salon da taje da shi wurin satar wanda za a iya cewa ba a taba gani ba.

Matar ta sace zinari a wani shagon da ake siyar da shi mai kimanin darajar naira miliyan daya da rabin.

Zinari
Bidiyo: An Kama Mata Ta Saci Zinarin N1.5m a Wani Shago da Salo Mai Bada Mamaki. Hoto daga Linda Ikeji
Asali: Facebook

Kamar yadda wani ma'abocin amfani da kafar sada zumunta ta TikTok mai suna @khaseem18 ya bayyana, matar ta sace zinarin tare da hadiye shi domin ta saukakewa kanta hanyar fitar da shi daga shagon ba tare da an cafke ta ba.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi

Sai dai kash, wannan shirin nata ya tashi a banza tunda an kama ta kuma har aka tsitsiyeta tare da tuhumarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yayin tuhumar, an ji matar tana rokon mai nadar bidiyon da kada ya wallafa hotonta a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

"Don Allah, kana da yara kaima. Don Allah kada ka wallafa ni a Facebook," ta dinga roko da harshen Yarabanci.

Ga bidiyon a kasa:

Kansar Bogi: Yadda 'Yan Damfara ke Amfani da Yarinya Mai Shekaru 9 Wurin Tatsar Miliyoyi Daga Jama'a

A wani labari na daban, Alexandria, wata yarinya karama mai shekaru 9 da ake yadawa tana fama da cutar kansa a bidiyoyin da suka karade kafafen sada zumuntar zamani ta bai wa jama'a tausayi.

"Ku taimaka min, bana son mutuwa," Alexander take cewa a bidiyon da aka wallafa a Facebook, YouTube da kuma tallar Google a manyan shafukan yanar gizo a duniya.

Kara karanta wannan

Wani Dan Najeriya Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Budurwar Sa Ta Nemi Auren Sa Da Kyautar Tsaleliyar Mota

Bidiyon yarinyar mai matukar taba zuciya mai shekaru tara ya nuna Alexandria tana neman taimako saboda iyayenta na kokarin hada kudin maganinta.

A take, hawaye ke zubowa daga idon yarinyar yana saukowa kan kumatun ta kuma tana sanarwa masu kallo cewa likitoci sun sanar da iyayenta cewa cutar kansa ta karade jikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel