Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamnan Gombe, Dankwambo Ya Yi Babban Rashi a Rayuwa
- Tsohon gwamnan Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya sanar da rasuwar dan uwansa, Alhaji Nasiru Mohammed Dankwambo
- Marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe bayan gajeriyar jinya, kamar yadda ɗan’uwansa ya bayyana
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga sanatan da iyalansa, tare da roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya rasa ƙaninsa, Alhaji Nasiru Mohammed Dankwambo.
Dankwambo ne ya sanar da rasuwar ɗan’uwan na sa, inda ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe bayan gajeriyar jinya.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan na jihar Gombe ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
'Dan tsohon gwamnan Arewa ya rasu bayan ya fito daga masallaci, an ji abin da ya faru
Dankwambo ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin
A cikin saƙon da ya wallafa, sanatan ya bayyana alhini kan rasuwar ƙanin na sa.
“Cikin tsananin baƙin ciki da jimami, ina sanar da rasuwar ƙanina, Alhaji Nasiru Dankwambo, wanda ya rasu a daren yau bayan gajeriyar jinya,” in ji shi.
Dankwambo ya kuma sanar da cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin, in Allah Ya yarda, ranar Litinin da ƙarfe 2:00 na rana a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.
Sanatan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya lullube marigayin da rahamarsa, Ya gafarta masa, Ya haskaka kabarinsa, sannan Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa ta ƙarshe.
Ya kuma roƙi Allah Ya ba iyalansa, ’yan’uwansa da abokansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa ta’aziyya
A nasa ɓangaren, Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan Sanata Dankwambo bisa rasuwar Nasiru Dankwambo.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Gwamna Abba ya fito ya gayawa Tinubu abin da zai samu a Arewa a 2027
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Litinin, Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi mai raɗaɗi.
Gwamnan ya ce rasuwar masoyi lokaci ne mai wahala ga iyalan mamaci, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga Sanata Dankwambo, daukacin iyalan Dankwambo da duk waɗanda ke jimamin rasuwar.
Ya ƙarfafa musu gwiwa da su samu ta’aziyya daga kyawawan halaye da abubuwan alheri da marigayin ya bari a rayuwarsa.
Gwamna Yahaya ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Delta ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Dakta Emmanuel Eweta Uduaghan, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 71 da haihuwa a duniya.
Emmanuel Uduaghan ya rasu ne a safiyar Litinin, 19 ga Oktoba, kamar yadda wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta nuna.
Asali: Legit.ng