'Yan ISWAP Sun Sha Wuta, Sojojin Sama Sun Soye Manyan Kwamandojinsu
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce wani hari ta sama da ta kai ranar 19 ga Oktoba, 2026, ya kashe manyan mayakan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.
- Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Jindullah, wanda aka bayyana a matsayin babban jami’in tsaron ƙungiyar, da Abul Kissa, mamba a majalisar shura ta ISWAP
- Harin ya lalata injinan kwale-kwale da babura da ake zargin ƙungiyar na amfani da su wajen zirga-zirga da gudanar da ayyukanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta kai wani hari na musamman da ta kai ta sama kan mayakan kungiyar ISWAP.
Rundunar sojojin ta ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
An rage mugun Iri: Yan ta'adda sun gamu da bala'in da ya fi karfinsu, sama da 100 sun mutu
Air Commodore Ehimen Ejodame ya bayyana harin a matsayin gagarumar nasarar soji da aka samu kan ’yan ta’adda a yankin.
Ya ce rundunar ta kai harin ne a wani sansanin ’yan ta’adda da ta gano a ranar 19 ga Oktoba, 2026.
An kashe Jindullah da Abul Kissa
A cewar Ejodame, binciken farko da aka gudanar bayan harin ya nuna cewa an kashe wasu fitattun mayakan ISWAP, ciki har da mutanen da ke da muhimmiyar rawa a tsarin tsaron ƙungiyar da majalisar shugabancinta.
Sanarwar ta ce daga cikinsu akwai Jindullah, wanda rahotanni suka bayyana a matsayin babban jami’in tsaron ƙungiyar kuma aminin Abu Saleem. Haka kuma, an kashe Abul Kissa, wanda yake cikin majalisar shura ta kungiyar ISWAP.
Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya lalata wasu kayayyakin sufuri da dabaru, ciki har da injinan kwale-kwale da babura da ake zargin ƙungiyar na amfani da su wajen zirga-zirga da gudanar da ayyukanta.
Rundunar ta ce harin zai rage ƙarfin ISWAP
Ejodame ya bayyana cewa aikin ya nuna yadda rundunar ke ci gaba da ƙoƙarin raunana hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda, katse jigilar kayayyakinsu da inganta tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ya ce rundunar na amfani da bayanan sirri wajen kai hare-hare na musamman kan sansanonin ’yan ta’adda da ke ɓoye a wurare masu wahalar isa.
A cewarsa, kashe manyan jami’an ƙungiyar da lalata muhimman kayayyakinta zai rage ƙarfin ISWAP na gudanar da ayyukanta, tare da takaita ikonta na tsara hare-hare da barazana ga al’ummomin da ke cikin haɗari.
Za a ci gaba da kai hare-hare
A nasa ɓangaren, babban hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da kai hare-hare masu ƙarfi kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassa daban-daban na Najeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa Sojin Saman Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran rundunonin soji da hukumomin tsaro domin ƙarfafa nasarorin da aka samu, kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Arewa maso Gabas.

Source: Original
'Yan ISWAP sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa akalla sojoji takwas sun mutu bayan motar sintirinsu ta taka nakiyar da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP suka binne a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kinuba, mai tazarar kilomita 25 daga Gamboru, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
Asali: Legit.ng

