'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Yana Zagin Kabarin Wata a Wani Faifan Bidiyo

'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Yana Zagin Kabarin Wata a Wani Faifan Bidiyo

  • Kafar TikTok na daya daga cikin kafafen da ke bari a yada nau'ikan bidiyo masu ban mamaki da sauran kafafe ba sa amincewa dasu
  • An ga wani matashi dan jihar Kano yana runtumawa mahaifiyar abokinsa ashariya saboda wani sabani da ya shiga tsakaninsu
  • Rundunar 'yan sanda ta bayyana yadda ta kamo matashin da tare fara yi masa tambayoyin don gano tushen matsalar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani mutum mai suna Abdullahi Yar Dubu biyo bayan wani faifan bidiyon TikTok da ya nuna yana zagi da ruwan ashariya a kan kabarin mahaifiyar abokinsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa an kama ‘Yar Dubu tare da mika shi zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Kano domin ci gaba da yi masa tambayoyi.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Yadda aka kame wani matashi da ya durawa kabarin mahaifiyarsa ashariya
'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Yana Zagin Kabarin Wata a Wani Faifan Bidiyo | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An ga ‘Yar Dubu a cikin faifan bidiyon yana tsaye a saman kabarin yana zagin mamaciyar da aka binne a wani lokaci a baya, rahoton Sahelian Times.

Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da ya tunzura matashin na aikata abin da bai dace ba, amma mafi yawan masu sharhi a shafukan sada zumunta sun nuna fushi da kin amincewa da maganganun nasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kuma ji ‘Yar Dubu a cikin faifan bidiyon yana kalubalantar abokin nasa da ya same shi a makabarta domin su fuskanci juna.

Martanin 'yan soshiyal midiya

Hausa Arewa Medium ta yada bidiyon a Facebook tare da bayyana labarin kawo 'Yar Dubu, kuma jama'a da dama sun yi martani game da maganganun matashin.

Ga dai abin da suke cewa:

@Al Mustapha Zainu ya ce:

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Dattawa Sun yi Magana a kan Yunkurin Radawa Kaduna Sabon Suna

"Masha Allah aigonda da akaka masa saboda abinda yayi yasaba ma addini mu kawai aimasa hukunci mai tsanani saboda idan wani yagani ba zaigodaba."

@Sadiq A Saidu ya ce:

"Masha Allah sunyi dai dai wlh nadade Banga tashin hankali irin wannanba Allah yasa mufi karfin zuciyarmu."

@Lawal Usman ya ce:

"Jahilci ciyo ne, Allah ka karemu daga sharrin son zuciya alfarma annabi."

@Fatima Adam ta ce:

"Kiji wata lukutar masifa mutum ya mutu ma baa kyaleshi ya kwanta lafiya ba to allah shi kyauta."

@Anas Iliyasu ya ce:

"Innalillahi wa inna ilaihirirraji, un,,wannan bashifa da hankali,,, dan daudu ne fa,,."

Garkuwa da mutane: Alkali ta yanke hukunci a kan Budurwar da tayi karyar an sace ta

A wani labarin, dazu wani karamin kotun majistare da ke zama a unguwar Wuse 2 a garin Abuja, ya saurari kara a kan wata Ameerah Sufyan mai shekara 23. Wannan Baiwar Allah ta kitsa labarin cewa an yi garkuwa da ita, alhali ba ta hannun ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Komai Ya Ji: Bidiyoyin Wata Zukekiyar Amarya Da Angonta Sun Haddasa Cece-kuce, Sun Hadu Matuka

A kan haka ne ‘yan sanda suka kai kararta a kotu. Rahoton da jaridar Punch ta fitar dazu, ya tabbatar da cewa Sufyan ta amsa laifin ta da bakinta.

Da ta bayyana a gaban Alkali Chukwuemeka Nweke a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni 2022, Ameerah Sufyan ta amsa duka zargin da suke wuyanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel