Wata Sabuwa: An Maka INEC Kara gaban Kotu kan N126bn
- SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin INEC da rashin yin cikakken bayani kan sama da N126.46bn
- Ƙungiyar ta nemi kotu ta tilasta wa INEC bayyana yadda aka kashe kuɗin, waɗanda suka amfana da su da kuma kamfanonin da suka karɓi kwangiloli
- Rahoton binciken kuɗaɗen gwamnati ya yi zargin an biya N112.15bn kan kayan zaɓe ba tare da bin ƙa’idojin sayen kayayyaki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP mai fafutukar kare haƙƙoƙin jama’a da tabbatar da ɗaukar nauyin masu riƙe da amana ta maka Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a kotu.
Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin INEC da gaza bayar da cikakken bayani kan sama da Naira biliyan 126.46 da aka ware wa ayyukan zaɓe.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2507/2026 ta nemi kotu ta bayar da umarnin mandamus, wanda zai tilasta wa INEC bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka kashe, aka yi amfani da kuma aka rarraba kuɗaɗen.
Kuɗaɗen sun haɗa da waɗanda aka ware domin sayen kayan zaɓe, na’urori, motoci da kuma gudanar da sauran ayyukan zaɓe.
SERAP ta nemi a bayyana waɗanda suka karɓi kuɗin
SERAP ta kuma nemi kotu ta tilasta wa hukumar zaɓen gabatar da cikakken bayani kan kuɗaɗen, tare da takardun da za su tabbatar da yadda aka gudanar da mu’amalolin kuɗin.
Ƙungiyar na son INEC ta bayyana adadin kuɗin da aka saki da waɗanda aka biya, sunayen waɗanda suka amfana da kuɗaɗen, da kuma kamfanonin da suka karɓi kwangiloli.
Ta kuma nemi a bayyana ainihin masu mallakar kamfanonin da suka karɓi kwangilolin, jaridar TheCable ta kawo labarin.
SERAP ta shigar da ƙarar ne bayan zarge-zargen da ke cikin rahoton binciken kuɗaɗen shekarar 2023 na Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya, wanda aka wallafa a ranar 7 ga Agusta, 2026.
Rahoton ya ce zarge-zargen sun shafi mu’amalolin kuɗi da aka gudanar tsakanin Janairu da Disamba 2022, yayin da wasu suka kai har zuwa 31 ga Disamba, 2023.
Zargin karya ƙa’idojin sayen kayayyaki
A cikin ƙarar da lauyoyinta, Kolawole Oluwadare, Kehinde Oyewumi da Andrew Nwankwo suka shigar, SERAP ta ce zarge-zargen sun haifar da manyan tambayoyi kan yadda hukumar zaɓen ke tafiyar da kuɗaɗen jama’a.
Ƙungiyar ta bayyana cewa lamarin ya fi tayar da hankali saboda nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora wa INEC da kuma muhimmancin kuɗaɗen wajen gudanar da tsarin zaɓen Najeriya.
A cewar SERAP, rahoton Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Gwamnati ya gano mu’amalolin kuɗi da dama da ake zargin an biya kuɗaɗen da suka kai biliyoyin naira ba tare da bin ƙa’idojin sayen kayayyaki ba.
Rahoton ya kuma nuna zargin rashin isassun hujjojin da za su tabbatar da cewa an kawo kayayyaki ko kuma an gudanar da ayyukan da aka bayar da kwangilolinsu.
Zargin biyan N112.15bn kan kayan zaɓe
A cewar ƙarar, ana zargin INEC ta biya Naira 112,155,597,845 domin sayen akwatunan zaɓe, na’urorin zaɓe da sauran kayayyaki ba tare da gudanar da gasa tsakanin masu neman kwangila ba.
SERAP ta kuma yi zargin cewa hukumar ba ta samu takardar shaidar amincewa daga Hukumar Kula da Sayen Kayayyakin Gwamnati (BPP) ba, wadda ake buƙata a irin waɗannan mu’amaloli.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta yi zargin cewa INEC ta biya Naira 1,058,925,000 domin sayen motocin Toyota Prado TXL na ƙirar shekarar 2021.
A cewar ƙarar, ba a yi tallar kwangilar ba, ko gudanar da gasa tsakanin masu neman ta, ko tantance tayin da aka gabatar. Haka kuma, ana zargin ba a samu takardar amincewa daga BPP ba.

Source: Facebook
An yi zanga-zanga a ofishin INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa mgoya bayan tafiyar Kwankwasiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano bayan hukumar INEC ta fitar sunayen yan takara.
'Yan Kwankwasiyyar sun gudanar da zanga-zangar lumana a Kano, suna neman INEC ta dawo da sunan ɗan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, cikin jerin sunayen ’yan takara.
Asali: Legit.ng


