Sanata Ya Tabbatar da Abin da Ake Tsoro a APC, Ya Ce Akwai Matsaloli cikin jam’iyyarsu

Sanata Ya Tabbatar da Abin da Ake Tsoro a APC, Ya Ce Akwai Matsaloli cikin jam’iyyarsu

  • Ali Ndume ya ce APC na fuskantar matsalolin cikin gida fiye da kalubalen da suke gani daga ’yan adawa
  • Ya goyi bayan fargabar da Kashim Shettima yake yi kan rikice-rikice da rashin haɗin kai a APC gabanin zabe
  • Shettima ya bukaci ’yan jam’iyyar su hada kai, su guji zagon kasa, Ndume yana tare da shi a wannan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ali Muhammad Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, ya goyi bayan kalaman Kashim Shettima kan batun APC.

Mai girma Mataimakin shugaban kasa ya koka cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar su ta APC mai rike da mulki.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima a taron City Boya a Abuja Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Ali Ndume yana tsoron rigimar cikin gidan APC

Ali Ndume ya fada wa tashar Arise APC na fuskantar matsaloli a cikin jam’iyyar fiye da wadanda ’yan hamayya suke fama da shi.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran gwamna ya watsa wa NDC kasa a ido da ya fice daga jam’iyya ana cikin kamfe

Ya ce yayin da jam’iyyun adawa na kara kaimi da nuna karfin hali gabanin zaben 2027, babban kalubalen APC shi ne rikicin gida.

Ya ce:

“Ina ganin Mataimakin Shugaban kasa ya fadi gaskiya ne kai tsaye. Muna da matsaloli da yawa a cikinmu fiye da wadanda ke wajenmu.”

Sanata Ndume ya kamanta 'yan siyasar Najeriya

Sanata Ali Ndume ya kara da cewa jam’iyyun siyasar Najeriya suna da kamanceceniya ta fuskar ’yan siyasar da sukeke cikinsu.

Ya ce yawancin bambance-bambancen da ke tsakaninsu sun samo asali ne daga neman mulki da jam’iyyar da mutum yake ciki.

Ya soki yadda ’yan siyasa suka fi mayar da hankali kan mutane maimakon manufofi, muhawara da hanyoyin magance matsalolin kasar.

A cewarsa, wannan na iya zama hadari saboda yana hana ’yan siyasa tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar jama’a.

Sanatan ya kuma zargi wasu ’yan siyasa da raina hankalin ’yan Najeriya, inda ya bukaci su mayar da hankali kan dabarun kawo gyara.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa 8 da suka bar APC sun canza shawara bayan haɗuwa da Shugaba Tinubu

Maganar Kashim Shettimaa ta tabbata a bakin sanatan

Vanguard ta ce kalaman Ndume sun biyo bayan gargadin da Kashim Shettima ya yi cewa sabanin cikin gida na APC sun fi damunsu.

Shettima ya fi tsoron wadannan matsaloli fiye da ’yan adawa gabanin zaben 2027.

‘Dan majalisar ya saba yin maganganu irin haka, ya na haska matslolin da ake fama da su a jam’iyya, gwamnati ko a fadar shugaban kasa.

Ali Ndume
Sanatan Borno, Ali Ndume Hoto: Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Bola Tinubu ya hadu da kungiyar 'dansa

An ji labari Bola Tinubu ya bukaci Seyi ya kara kokari wajen jan matasa, ya ce yana bin sawunsa har ya yi ba'a cewa zai yi takara.

Seyi Tinubu shi ne jagoran kungiyar City Boy Movement wanda ta gana da shugaban kasa a kokarin ganin ya zarce a kan mulki a 2027.

Shugaban kasa ya ce yaron shi zai gaje shi a siyasa, ya bukaci matasa su yi koyi da shi saboda ganin yadda yake yi wa kasa hidima

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng