Magana Ta Yi Girma An Kai Yaron Ministan Tinubu Kotu a Badakalar Filin $2m a Abuja

Magana Ta Yi Girma An Kai Yaron Ministan Tinubu Kotu a Badakalar Filin $2m a Abuja

  • Wani ɗan kasuwa ya zargi ɗan Nyesom Wike da karɓar dala miliyan 2.1 domin samo masa filaye a Abuja
  • Ya ce Jordan Wike ya yi ikirarin cewa mahaifinsa ya amince da yarjejeniyar, amma bai cika alƙawarin ba.
  • Jordan ya musanta zargin, yayin da EFCC ta karɓi ƙarar domin bincike a ƙarshe yanzu sun ƙare a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Wani ɗan kasuwa, Safwan Garba, tare da kamfaninsa na GY Global Oil & Gas Nigeria Limited, sun kai wata kara gaban EFCC.

Sun shigar da ƙara ga Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC), suna zargin Jordan Nyesom-Wike da aikata laifuffuka.

Jordan Wike
Jordan Wike da mahaifinsa, Ministan Abuja Hoto: Micheal Oladipupo Enoch/EFCC
Source: Facebook

Yaron Nyesom Wike yana fuskantar zargin badakala

Rahoton da aka samu a The Cable ya ce ‘dan kasuwan da kamfaninsa suna zargin ɗan Ministan Birnin Abuja, Nyesom Wike, da laifin damfara.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Masu ƙarar sun yi zargin cewa Jordan ya ce yana da masaniya da amincewar mahaifinsa wajen taimaka musu su samu wasu filaye a Abuja.

A ƙarar da suka shigar a ranar 11 ga Disamba, 2025, sun ce Jordan ya yi musu alƙawarin samo musu filaye masu girman hekta 30 a Katampe.

Haka zalika sun ce ya yi alƙawarin nemo masu wasu hekta 30 a Guzape duk a Abuja.

Sun ce ya tabbatar musu da cewa yana yawan taimaka wa mutane wajen samun filaye, kuma mahaifinsa na goyon bayan wannan aiki da yake yi.

Zargin da ake yi wa Jordan Wike

Masu ƙarar sun zargi Jordan da damfara, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, karkatar da abin da aka ba shi da kuma yin amfani da su ba bisa ƙa'ida ba.

Sun ce ya karɓi dala miliyan 2.1 domin taimaka musu samun filayen a birnin Abuja.

A cewar takardar ƙarar, Jordan ya ƙara ƙarfafa ikirarinsa ta hanyar kiran mahaifinsa ta waya a gaban ɗan kasuwar domin sanar da shi maganar.

Kara karanta wannan

'Dan tsohon gwamnan Arewa ya rasu bayan ya fito daga masallaci, an ji abin da ya faru

Masu ƙarar sun ce Jordan ya nemi dala miliyan biyu a matsayin kuɗin da zai miƙa wa mahaifinsa, Ministan Abuja, domin su mallaki filayen.

Sun kuma zargi Jordan da karɓar ƙarin $100,000 a matsayin kuɗin hidimarsa na kansa.

A cewar su, an biya kuɗin gaba ɗaya a ranar 17 ga Oktoba, 2025, a tsabar kuɗi amma babu filaye, sai ga shi yanzu ya daina amsa kiransu.

Sun yi hujja da cewa Adamu Sani da Aliyu Sarki sun zo a matsayin shaidu lokacin da aka biya dalolin.

Sun ce Jordan kuma ya zo tare da wani mutum mai suna Onor Sandy, wanda ya gabatar da shi a matsayin abokinsa kuma abokin hulɗarsa.

Masu ƙarar sun ce Jordan ya yi alƙawarin kammala aikin samar da filayen cikin wata ɗaya. Amma bayan ya karɓi kuɗin, bai cika alƙawari ba.

Sun ce lambar wayar Birtaniya da ya ba su ba ta shiga, kuma duk ƙoƙarin da suka yi na samun sa, har ta hannun mutanen da suka san ministan.

An bukaci EFCC ta kama yaron Wike

Saboda haka, sun buƙaci EFCC ta fara bincike cikin gaggawa, ta kama Jordan domin yi masa tambayoyi, sannan ta gurfanar da shi idan ta kama.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya jawo wa mawaki Davido matsala da ya goyi bayan Tinubu

Leadership ta ce suna neman a dawo masu da kudinsu $2.1m kuma a kara masu da diyyar N100m.

Da yake magana da manema labarai a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Litinin, Ibrahim Waru, ya ce ba a yi komai ba don haka sun zo kotu.

Sai Disamba kotu za ta cigaba da zama

Lauyan masu ƙarar, ya ce EFCC ta tabbatar musu da karɓar ƙarar amma har yanzu ba ta ɗauki mataki ba.

A halin da ake ciki, rahoton ya ce mai shari'a Silvanus Oriji ya ɗage ci gaba da sauraron wannan kara sai zuwa ranar 1 ga watan Disamba, 2026.

Shi kuma Jordan ya musanta zarge-zargen, inda ya shaida wa kotun cewa ba ya Najeriya a ranar da masu ƙarar suka ce sun ba shi makudan kuɗin.

Wikes
Ministan Abuja, Nyesom Wike da yaransa Hoto: Sam Ovbigho Omogor
Source: Facebook

Nyesom Wike da Gwamnan Imo sun yi wa junna raddi

An ji labari taron rantsar da kwamitin kamfen Bola Tinubu ya zama wajen habaici tsakanin Nyesom Wike, Godswll Akpabio da Hope Uzodimma.

Ministan Abuja, Wike ya kalubalanci gwamnonin APC su tabbatar da nasarar Tinubu a jihohinsu duk da cewa shi 'dan jama'iyyar PDP mai adawa ne.

Kara karanta wannan

"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Shi kuma Akpabio ya yi gargaɗi kan neman mukamai, yayin da Uzodimma ya jaddada goyon bayan dukkan ’yan takarar APC da aka tsaida a jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng