Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu

Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu

  • Musa Sani, dan Najeriya da ya yi fice bayan kwaikwayi gadar saman Maiduguri ya kammala wani sabon aiki mai tsananin kyau
  • Dan baiwan wanda Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya baiwa tallafin karatu ya kammala aiki kan wata dankareriyar gadar sama da ya kwaikwaya
  • Musa ya yi amfani da laka da fenti masu kaloli wajen zana wannan sabon aiki wanda hotunan suka yadu a shafukan soshiyal midiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - Musa Sani, dan asalin jihar Borno mai shekaru 13 wanda ya kwaikwayi irin gadar saman Maiduguri ya sake kera wani da ya burge yan Najeriya.

Sabbin hotunan da Onivwo-Omasoro Ali Ovie ya yada a Twitter ya nuna cewa yaron ya sake kera gadar sama mai girma da hanyoyi da dama.

Gadar sama
Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu Hoto: @OvieNews
Asali: Twitter

Gadar sama na biyu da Musa Sani ya yi

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

A cewar wallafar da aka yi a Twitter, yaron ya yi amfani da jar laka da fenti wajen cimma wannan aiki da ya ja hankalin mutane da dama kuma ya burge su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake yada hotunan a Twitter, Onovwo ya rubuta:

“Musa Sani ya sake kera wata gadar sama ta hanyar amfani da jar laka da fenti. Musa ya kasance dan Borno wanda ya kera irin gadar sama da Zulum ya yi a Maiduguri.”

Musa ya yi suna ne bayan kera gadarsa ta farko kuma ya ja hankalin Gwamna Zulum.

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Zubairumakeri ya ce:

“Ya kamata a yi da hazakar da Allah ya yi masa sannan a karfafa masa gwiwa. Na ji dadi cewa Gwamna ya je da kansa don ganinsa sannan ya bashi tallafin karatu. Na yaba matuka da kaifin basirar Sani.”

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

@EmemEmemussoro ya yi martani:

“Yadda Allah ke raba rahamarsa ba zai fadu ba. Ka yi tunani da ace wannan yaron daga gidan masu kudi ya fito. Ina rokon Allah yasa masu kudin garinsa su taimaka masa. Zai amfane su a nan gaba kadan.”

@Prostinator ya ce:

“A watan Fabrairu ya kaddamar da gadar sama na farko sannan gamu a Agusta ya sake kaddamar da wani ta hanyar amfani da laka kuma, ya kamata a yaba da wannan kokari nasa.”

Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri

A baya mun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bada Naira miliyan 5 ga wata makaranta mai zaman kanta domin daukan nauyin karatun Musa Sani, yaro dan shekara 13 mai hazaka a Borno wanda ya yi amfani da laka ya kwaikwayi ginin gadan sama ta farko a jihar da ke custom round about a Maiduguri.

Kara karanta wannan

A Yafe Min: Lalong Ya Roki Cocin Katolika Kan Tuntuben Harshe Da Ya Yi Na Tsoma Paparoma A Siyasar Najeriya

An biya kudin ne ga hukumar makarantar Golden Olive Academy, Maiduguri, domin daukan nauyin karatun Musa daga ajin frimare na hudu har kammala babban sakandare, Nigerian Tribune ta rahoto.

Iyayen Musa, dan ajin frimare na 3 Community School da ke Gwange a Maiduguri, ba masu hannu da shuni bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel