Hotunan Kyakkyawar Budurwar Da Ta Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Arewacin Amurka, Ta Samu Kyaututtuka

Hotunan Kyakkyawar Budurwar Da Ta Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Arewacin Amurka, Ta Samu Kyaututtuka

  • Kyakkyawar budurwa Fartun wako ta lashe gasar karatun Al-Kur'ani mai girma na Imam Shatibi da aka yi a Arewacin Amurka
  • Fartun ta samu manya-manyan kyaututtuka da suka hada da hadaddiyar mota kirar 2022 Toyota Highlander da kuma kujerar Umrah
  • An gudanar da gasar na 2022 a makarantar Kennedy da ke Bloomington, Minnesota inda Fartun ta zo ta daya

Wata matashiyar budurwa mai suna Fartun wako ta lashe gasar karatun Al-Qur’ani na Imam Shatibi inda ta zo ta daya.

Sakamakon wannan bajinta da kyakkyawar budurwar ta yi an bata kyautar dankareriyar mota kirar 2022 Toyota Highlander sabuwa fil, kudi da kuma kujerar zuwa aikin Umrah.

Kamar yadda shafin Converts to Islam ya wallafa a Facebook, sama da dalibai 530 ne suka shiga gasar a wannan shekarar.

Fartun
Hotunan Kyakkyawar Budurwar Da Ta Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Arewacin Amurka, Ta Samu Kyaututtuka Hoto: Converts to Islam
Asali: Facebook

Fartun wacce ta wakilci Minnesota ta lashe gasar karatun Al-Kur’anin mai girma na Arewacin Amurka wanda aka yi a karo na takwas a makarantar Kennedy da ke Bloomington, Minnesota.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba wannan ne karo na farko da matashiyar budurwar ke yin nasara a gasa ba domin ita ce ta zo ta biyu a gasar karatun Al-kur’ani da aka yi a Toronto a 2019.

Hakazalika ta kasance mahaddaciyar Al-Kur’ani mai tsarki.

Jarumar kasar Ghana, Akuapem Poloo Ta Karbi Addinin Musulunci

A wani labari na daban, Shahararriyar jarumar kasar Ghana Rosemond Alade Brown wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta karbi addinin Musulunci.

Poloo ta Musulunta ne a ranar Talata, 9 ga watan Agusta, bayan ta yi kalmar shahada tare da kadaita Allah.

Jarumar da kanta ce ta sanar da labarin Musuluntar tata a shafinta na Instagram inda ta wallafa hotunan dan kwarya-kwaryan taron da aka shirya na Musuluntarta tare da wasu malamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel