Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami

Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami

  • Daga wasa wani matashi mai shgekaru 19, Eyinatayo Iluyomade, wanda ke wasan barkwanci ya tsinci kansa a gidan kurkuku
  • Iluyomade ya ajiye wata takarda a banki inda ya yi masu barazana cewa shi da yan kungiyarsa za su zo yin fashin da makami
  • Hakan ya sanya dukkanin bankunan da ke aike a Ondo rufewa a wannan ranar saboda tsoron kawo masu farmaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Wani matashi dan shekaru 19 mai wasan barkwanci a Lagas, Eyinatayo Iluyomade, ya tsinci kansa a kurkuku bayan ya yi wasan barkwanci mai tsada ta hanyar ajiye wasikar fashi da makami a wani bankin zamani da ke garin Ondo, jihar Ondo.

Yan sanda sun gurfanar da Iluyomade a gaban kotu kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, barazana da kuma tin abubuwan da za su iya kawo barazana ga tsaro, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Dan sanda mai kara, Akao Moremi, ya fada ma kotu cewa wanda ake kara ya ajiye wata takarda a bankin yana nuna cewa da misalin karfe 1:00pm na wannan rana, mambobin kungiyarsa na fashi da makami za su zo yin fashi a bankin.

Sandar kotu
Daga Wasa: Allkali Ya Aike Da Mai Wasan Barkwanci Gidan Maza Kan Firgita Banki Da Wasan Fashi Da Makami Hoto: Thisdaylive
Asali: UGC

Moremi ya ce takardar ya kasance barazanar tsaro ga bankin FirstBank reshen Sabo, a garin Ondo kuma ya tilastawa dukka bankuna da ke aiki a Ondo rufewa tsawon wannan rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake karan bai amsa tuhumar da ake masa ba.

Amma lauyen wanda ake kara, Hawkins Akinnugba, ya nemi a bayar da belin wanda yake karewa tare da sharudda.

Sai dai kuma, mai gabatar da kara na yan sanda ya yi adawa da bukatar neman belin yana mai cewa wanda ake karan zai kawo karan tsaye a yayin binciken lamarin domin akwai wasu masu laifi da ke da hannu a barazanar.

Kara karanta wannan

Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

Rahoton ya kuma kawo cewa Mai shari’a a kotun, Mosunmola Ikujuni, ta ki bayar da belin har zuwa lokacin da za a kamo sauran masu laifin.

Ikujuni ta ce:

“Idan a ranar zama na gaba, wanda ke gabatar da karan bai kama dukka sauran masu laifin da ke da hannu a lamarin ba, toh kotun za ta yi abun da ya dace.”

Daga nan sai ta dage zaman don yanke hukunci kan bukatar bayar da belin.

Wanda ake karan ya kuma fada ma kotu cewa shi mai wasan barkwanci ne kuma cewa takardar da ya ajiye a bankin wasan barkwanci ne, yana mai cewa yana ta aikata irin haka a Lagas har zuwa lokacin da ya dawo garin Ondo.

A cewarsa:

“Wannan shine karo na farko da nake yin wasan barkwanci a Ondo.
“Babu wasu sauran gungun yan fashi da suka so kai farmaki bankin kamar yadda aka rubuta a takardar.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Don haka Iluyomade ya roki kotu da ta yafe masa sannan ya yi alkawarin ba zai sake irin wannan wasan ba.

Matashi Ya Sha Mamaki Bayan Ya Gano 'Yar TikTok Ta Yi Amfani Da Hotonsa Matsayin Marigayin Kawunta

A wani labarin kuma, wani matashin dan Najeriya mai suna Chima ya cika da mamaki bayan ya gano cewa wata ‘yar TikTok ta yi amfani da hotunansa a shafinta, inda ta yi ikirarin cewa shi din kawunta ne da ya mutu kwanan nan.

‘Yar TikTok din ta yi amfani da hotunan Chima wajen tsara wani bidiyo dauke da rubutun da ke nuna cewa shi din ya mutu.

Matashin ya je shafinsa na Twitter domin nuna takaicinsa a kan wannan abu da ‘yar TikTok din ta yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel