Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka

Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka

  • Wani Ba'indiye daga yankin Bihar, Dharamdev Ram, ya shafe tsawon shekaru 22 ba tare da ya yi wanka ba
  • Ram mai shekaru 62 a duniya ya sha alwashin cewa ba zai sake yin wanka ba har sai an daina cin zarafin mata, kashe dabbobi da kuma kawo karshen rigingimun filaye tsakanin maza
  • Duk da wannan hali da yake ciki, mutanen kauyensa wadanda suka tabbatar da rashin wankan nasa suna mutunta shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Indiya - Dharamdev Ram, ya kasance tsoho mai shekaru 62 daga yankin Bihar a kasar Indiya kuma ya shafe tsawon shekaru 22 ba tare da ya yi wanka ba.

Al’ummar kasar Indiya sun yi martani bayan samun wannan labari na rashin wankan Ram, Aminya ta nakalto.

Ram dai ya yi suna sosai a kauyensa na Baikunthpur, inda kowa ya san cewa baya sanyawa kowani bangare na jikinsa ruwa tsawon shekaru 22.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Tsoho
Hotunan Tsoho Mai Shekaru 62 Wanda Ya Yi Shekaru 22 Ba Wanka Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Dalilin da yasa Ram ya daina wanka

Duk da sanin halin da tsohon ke ciki, babu wani mutum da ke yi masa ba’a ko ya zolaye shi a kan wannan lamarin, sai dai ma girmama shi da ake sosai a kan wannan hukunci da ya daukarwa kansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dattijon dai ya sha alwashin cewa ba zai sake yin wanka ba har sai an daina cin zarafin mata tare da kawo maslaha a kan rigingimun filaye tsakanin maza da kuma kawo karshen kashe dabbobin da ba su ji ba ba su gani ba.

Ganin ba a kawo karshen wannan lamari bane ya sanya Ram ci gaba da tsare alkawarin da ya daukarwa kansa.

Da yake zantarwa da kafar labarai ta ETV Bharat, Ram ya ce:

“A 1975, na yi aiki a wata masana’anta a Jagdal da ke Bengal, sannan na yi aure a 1978 kuma ina rayuwa yadda ta kamata. Amma a 1987, sai na gane cewa ricicin filaye, da kashe-kashen dabbobi da cin zarafin mata ya fara hauhawa. Don haka a kokari na neman amsa, na tunkari wani ‘Guru’ wanda ya dauke ni a matsayin almajirinsa sannan ya daura ni kan tafarkin ibada. Tun daga lokacin na bin tafarkin ibada sannan na fara zantawa da abin bautana Rama.”

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

A shekarar 2000, Ram ya yi murabus daga aiki a masana’antar sannan ya koma gidansa amma daga bisani ya sake komawa saboda matsin lambar da yake samu daga iyalinsa.

Bayan ya yanke shawarar daina cin abinci da wanka lokacin da manajan kamfanin ya samu labari, sai yak ore shi sannan ya koma gidansa.

Matarsa mai suna Maya Devi ta mutu a shekarar 2003, kuma ko a lokacin bai yi wanka ba.Daga bisani daya daga cikin ‘ya’yansa maza ya mutu amma ya ci gaba da rike alkawarinsa.

Da aka yi bincike, mazauna kauyen nasu sun tabbatar da ikirarin na Ram.

“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

A wani labarin, wani dan Najeriya mazaunin Ingila ya je shafin soshiyal midiya don nuna wani bidiyonsa yana tafiya shi kadai a titi.

Mutumin wanda ke alfahari da kansa ya ce titunan sun zama wayam ne saboda duk Turawa sun gudu saboda tsoron zafin rana.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Da yake magana a cikin harshen Igbo, mutumin wanda ke amfani da shafin TikTok ya ce shawarar da gwamnatin Ingila ta baiwa al’ummar kasar shine ya sa unguwanni da tituna suka yi wayam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel