Permanent Day: Yadda Magidanta Suka Kirkiro Sabuwar Hanyar Dallowa Uwargida Kishiya Babu Saninta

Permanent Day: Yadda Magidanta Suka Kirkiro Sabuwar Hanyar Dallowa Uwargida Kishiya Babu Saninta

  • Magidanta a jihar Adamawa sun bullo da sabon salon karin aure da suke kira da Permanent Day inda suke aure babu sanin uwargida
  • Suna yin auren ne wasu lokuta da sanin danginsu inda zasu dinga wuni kadai a gidan amarya, amma kwana a gidan uwargida
  • Da yawa daga cikin magidanta da suka yi irin auren sun ce suna jin dadinsa, sai dai 'yan mata basu cika yadda a yi irin wannan auren da su ba

Adamawa - Magidanta a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya sun kirkiro da wata dabarar dallowa uwargida kishiya ba tare da saninta ba.

Bincike ya nuna yadda magidanta a jihar Adamawa suka rungumi wannan salon mai suna "Permanent Day" inda suke yin karin aurensu salamun kaulin ba tare da uwargida ta tada hazo ba.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

Amarya
Permanent Day: Yadda Magidanta Suka Kirkiro da Sabuwar Hanyar Dallowa Uwargida Kishiya Babu Saninta. Hoto daga DW Hausa
Asali: Facebook

Kamar yadda DW Hausa ta ruwaito, tace wannan tsarin aure na Permanent Day wani tsari ne da magidanta ke yi. Ana yin auren ba tare da sanin uwargida ba, wani lokacin kuwa har da 'yan uwan ango ake hada baki.

A wannan tsarin, mijin na wuni ne kadai a gidan amarya ba tare da kwana ba. Da yawa daga cikin magidantan da suka yi wannan salon karin auren kuwa sun ce sun ji dadin shi matuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me magidanta suke cewa a kai?

"Na jima ina da bukatar in yi mata biyu, amma matata duk hanyar da na bullo da yin wannan auren sai ta wargaza shi ta hanyar da na sani da wacce ban sani ba.
"Yanzu haka wannan auren da nayi ina jin dadinsa saboda ina zaman lafiya da wacce na aura. Don ina ganin ma gara da nayi wannan auren na permanent day akan irin wanda za a yi na cewa ita uwargida ta san tana da kishiya, ita ma amarya haka," cewar Malam Sani, wani magidanci da yayi wannan salon karin auren.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

Me mata suke cewa a kai?

Duk da dai 'yan mata basu cika yarda da wannan salon na karin aure da su ba, wata ta bayyana cewa auren take so ba biki ba, shine dalilinta na amincewa a yi wannan auren da ita.

"Gaskiya wannan tsarin auren na Permanent Day abu ne mai matukar muhimmanci musamman ga irinmu. Saboda wanda na aura, ina son shi yana so na amma matarsa ta dage cewa ba zata taba bari ya kara mata kishiya ba.
"Sai ya kawo shawarar cewa mu yi wannan tsarin auren. Toh na ga babu wani aibu tunda yadda za a daura aure kamar yadda addini ya tanada haka za a yi. Kawai dai kwana ne ba zai dinga yi wurina ba.
"A gaskiya ina jin dadin aurena kuma ina kallon kaina kamar yadda kowacce matar aure take haka nake," cewar Farida Usman, amaryar Permanent Day.

Mece ce makomar irin wannan auren a addinin Islama?

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

Dr Bashir Imam, wani malamin addinin Musulunci a jihar Adamawa yayi karin bayani kan matsayar wannan auren.

"Matukar an cika ka'idojin addini wurin yin wannan aure, ya halasta a yi wannan auren da ake kira da permanent day. Saboda ba dole bane mutum sai ya samu izinin uwargidansa kafin ya kara aure ba.
"Amma yana da kyau a matsayin kyautatawa ya sanar da ita. Batun yayi dare a wurin wance, yini a wurin wance, idan sun yarda da shi basu tauyewa kowa hakki ba.
"Sai dai kada mace ta kuskura miji ya aureta babu wanda ya sani. A yi komai a rubuce, ya aureta a ranar kaza, limami kaza ya daura da sauransu ga kuma shaidu."

Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa

A wani labari na daban, birnin Sokoto zai dauka manyan baki inda ake sa ran zai cika dankam da jama'ar da zasu halarci daurin auren 'dan Sarkin kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, Kabiru Aminu Bayero da dalleliyar amaryarsa Aisha Ummarun Kwabo.

Kara karanta wannan

Matan Da Suka Ki Amincewa Da Tayin Auren Maza Za Su Fara Biyan Tara A Chadi

Tuni dai shirin wannan bikin na 'yan gata ya kankama inda har aka yi hotunan kafin bikin na amarya da ango cike da izza tare da bayyanar al'adun sarauta.

A hotunan da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga jinin sarauta tare da zukekiyar amaryarsa sun cakare gwanin sha'awa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel