Babbar Magana: Gwamna Abba Ya Fito Ya Gayawa Tinubu Abin da Zai Samu a Arewa a 2027
- Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da goyon bayan Arewa ga burin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takara a zaɓen 2027
- Gwamnan ya ce Kano za ta jagoranci sauran jihohin Arewa wajen ƙarfafa fitowar masu kaɗa ƙuri’a ga Tinubu
- Ƙungiyar Arewa for Asiwaju, ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, na son tallata ayyukan Tinubu da tattara goyon baya ga tikitin Tinubu da Shettima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tabbaci kan zaben 2027.
Gwamna Abba ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa Arewa za ta mara masa baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa , Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2026 a shafinsa na Facebook.
A cikin sanarwar, Gwamna Abba ya ce Arewa na da yakini kan Tinubu kuma ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa burinsa na yin wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa.
Buɗe ofishin A4A ya nuna aniyar Arewa
Gwamnan ya bayyana cewa ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) a Abuja ya ƙara nuna aniyar yankin Arewa na tallafa wa Tinubu a zaɓen 2027.
A cewarsa, ƙungiyar za ta tattara goyon baya a faɗin jihohin Arewa tare da ƙarfafa hulɗar siyasa gabanin babban zaɓen da ke tafe.
Abba ya ce kano za ta jagoranci tattara ƙuri’u
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana Kano a matsayin jihar Arewa da ke samar da mafi yawan ƙuri’u, yana mai cewa za ta jagoranci sauran jihohin yankin wajen ƙara yawan masu fitowa zaɓe domin kaɗa ƙuri’a ga Tinubu.
Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa Kano za ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar da shugaban ƙasar ke nema a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Shin Tinubu ya karya doka da ya ce ba zai je kamfe wasu jihohin Najeriya ba? An samu bayani
Badaru Abubakar ne ke jagorantar ƙungiyar A4A
Ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wadda tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ke jagoranta, na da manufar tallata ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma tattara goyon baya ga tikitin Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027.
Shugaba Bola Tinubu dai na neman sake darewa kan madafun ikon Najeriya a karo na biyu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Facebook
Buhari ya hango illar da Tinubu zai yi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fahimci illar da Bola Ahmed Tinubu zai iya yi wa Najeriya shi yasa ya kokarin hana shi zama magajinsa.
Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi kokarin dakile duk wata matsin lamba kan Tinubu ya gaje shi saboda ya san zai cutar da Najeriya.
Shugaban na PRP ya kuma zargi Tinubu da kai Najeriya matakin da ba ta taɓa kai wa ba na tabarbarewa a ƙarƙashin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng
