Ina Ganin Wayarsa, Son shi ya Fice Daga Raina: Budurwa Ta Bayyana Dalilin Tsanar Masoyinta

Ina Ganin Wayarsa, Son shi ya Fice Daga Raina: Budurwa Ta Bayyana Dalilin Tsanar Masoyinta

  • Wata budurwa 'yar Najeriya ta janyo cece-kuce bayan ta sanar da dalilin da yasa mutumin da ta fara so ya fice mata daga zuciyarta
  • Kamar yadda tace, ta fara son shi daga dora ido a kan shi amma soyayyar ta bace bayan ta ga bayan wayarsa
  • Ta dinga dariyar yadda yake rike da iPhone mai abubuwan latsawa, abinda tace ya kashe soyayyarsa da ta fara yi masa baki daya

Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayyana yadda wayar wani matashi ta sa soyayyarsa ta fice daga zuciyarta baki daya.

A wani bidiyon TitTok, budurwar ta rubuta cewa lokacin da ta fara ganinsa ta ji tana kaunarsa amma kaunar ta bace bayan ta ga yana amfani da waya kirar IPhone amma mai abubuwan latsawa.

Budurwa
Ina Ganin Wayarsa, Son shi ya Fice Daga Raina: Budurwa Ta Bayyana Dalilin Tsanar Masoyinta. Hoto daga TikTok/@kateapril21
Asali: UGC

A tantancewarta, duk namiji dake amfani da iPhone mai madannai, bai dace da ita ba kuma ya kwafsa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

Tace ta gane irin wayar da yake rike da ita ne bayan ta ga bayan wayarsa yayin da ya daga ta zai yi wani abu, yana latsawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Budurwar ta nadi bidiyon matashin ba tare da ya sani ba. A yayin kare kanta daga caccakar da aka dinga yi mata, a karkashin wallafarta tace:

"Matashin har yanzu iPhone yake amfani da ita amma ta latsawa."

Kalla bidiyon a kasa:

An dinga yi mata martani

Video Loner yace:

"Toh fah, ashe har da yanayin wayar da mutum ke rikewa ake gane kudinsa. Da haka wasu mazan ke amfani da dukkan kudinsu suna siyan 12 pro max."

Hucholife yace:

"Ina amfani da 7plus amma ina samun abincin ci sau uku fiye da mai amfani da kamarori uku."

Sposh6 yace:

"Tun farko saurayin ma bai miki ba. Don haka bai kamata ma ki damu da lamarinsa ba. Idan kuma kina jin kina da kudi, ki siya ki bashi."

Kara karanta wannan

Bidiyo: An Kama Mata Ta Saci Zinarin N1.5m a Wani Shago da Salo Mai Bada Mamaki

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa kyakyawa a TikTok wacce ke aiki matsayin 'yar aiki a Dubai tayi bidiyo inda take yi wa masu mata dariya martani.

Tace mutane suna mamakin dalilin da yasa take 'yar aikin gida a Dubai duk da zata iya samun kudi da irin diri da surar da take da shi.

A martanin jama'a kan ra'ayinta akan aikin da take yi, budurwar ta bayyana cewa bata damu ba kuma ta mayar da hankali kan abinda ya kai ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel