Gwamna Radda Ya Kawo dalilin da Ya Sa ’Yan Katsina Za Su Hada Kai Su Zabi Tinubu

Gwamna Radda Ya Kawo dalilin da Ya Sa ’Yan Katsina Za Su Hada Kai Su Zabi Tinubu

  • Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya bayyana cewa jihar za ta goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Radda ya ce sarakunan gargajiya da tawagar Abdulaziz Yari ta ziyarta sun nuna goyon baya ga Tinubu
  • Gwamnan ya ce Tinubu ya daɗe yana tallafa wa siyasar Katsina, kuma yana da kyakkyawar alaƙa da tsofaffin shugabannin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce jihar za ta goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Radda ya danganta matsayar jihar da dadaddiyar alaƙar siyasa tsakanin Tinubu da shugabannin Katsina, da kuma yadda shugaban ƙasar ke tallafa wa muradun jihar.

Katsina za ta sake goyon bayan Tinubu
Marigayi Muhammadu Buhari da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake karɓar wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Sanata Yari ya ziyarci sarakunan gargajiya

Yari ya ziyarci Katsina domin neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu, inda ya kuma kai ziyara masarautun Katsina da Daura a wani ɓangare na shirin wayar da kan jama’a.

Sanata Yari bai yi tsokaci kan dalilin ziyarar tasa ba, amma Radda ya ce tawagar ta kammala ganawa da sarakunan gargajiya domin neman goyon bayansu ga Tinubu gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan ya ce:

“Ya zo ne domin neman ƙuri’u. Ya zagaya ya ziyarci hukumomin gargajiya domin bayyana musu manufa da hangen nesa na shugaban ƙasa da kuma abin da yake son yi wa wannan ƙasa.
“Mun tabbatar musu cewa za mu yi ƙoƙarin ganin shugaban ƙasa ya yi nasara a zaɓen 2027, in Allah Ya yarda.”

Radda ya bayyana kwarin gwiwar cewa ganawar da aka yi za ta haifar da goyon bayan jama’a ga shugaban ƙasar a zaɓe mai zuwa.

Radda ya ce Katsina ta Tinubu ce
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Yadda sarauna za su goyi bayan Tinubu

Kara karanta wannan

Yan Majalisa 8 da suka bar APC sun canza shawara bayan haɗuwa da Shugaba Tinubu

Gwamnan ya bayyana yadda aka tarbi tawagar a matsayin abin ƙarfafa gwiwa, yana mai cewa mazauna jihar sun nuna kyakkyawar amsa ga yaƙin neman sake zaɓen Tinubu.

Ya ƙara da cewa sarakunan gargajiyar da tawagar ta ziyarta sun nuna goyon baya ga Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin ɗan jihar.

Radda ya ce:

“Abin ya kayatar sosai, kuma sun gani da kansu. Katsina ta nuna kyakkyawar amsa wajen goyon bayan shugaban ƙasa.
“Sun nuna goyon bayansu, kuma sun yi alƙawarin biyayya ga shugaban ƙasa. Suna ɗaukar shugaban ƙasa a matsayin ɗan gida.”

Da yake bayanin tushen alaƙar siyasar Tinubu da Katsina, Radda ya ce shugaban ƙasar ya daɗe yana tallafa wa muradun siyasar jihar tare da kyakkyawar alaƙa da fitattun shugabanninta.

A cewar gwamnan, Tinubu ya goyi bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya fito daga Katsina, sannan yana da kusanci da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.

Radda ya ce:

“Ya kasance abokin siyasa ga marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua. Saboda haka, Katsina gida ne a gare shi, kuma ya zo ne domin sake tabbatar mana da hakan.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya shirya kayar da Tinubu a jihohi 12 a zaben shugaban ƙasa na 2027

'Ayyuka na sun wadatar': Radda kan zaben 2027

Mun ba ku rahoto cewa Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce zai nemi wa’adi na biyu ne bisa ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar, ba sababbin alkawura ba.

Radda ya bayyana cewa dukkan mazabu 361 na jihar Katsina sun amfana da akalla wani aiki ko shiri na gwamnatinsa.

Gwamnan ya bukaci shugabannin APC Zalla Movement su karfafa wayar da kan jama’a da kuma yakin neman zabe a matakin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.