Mai Kamar Maza: An Gano Budurwa Yar Shekaru 26 Da Ke Tuka Tankar Mai, Hotunanta Sun Yadu

Mai Kamar Maza: An Gano Budurwa Yar Shekaru 26 Da Ke Tuka Tankar Mai, Hotunanta Sun Yadu

  • An gano wata matashiyar budurwa yar Najeriya tana tuka motar tankar mai, sai wani mutumi ya yada hotunanta a Twitter saboda tsananin mamaki
  • An gano budurwar mai suna Yemi tsaye kusa da motocin tanka a cikin hotunan wanda @bjyomyom ya wallafa a Twitter
  • Gaba daya ana yiwa tukin tanka kallon aikin maza kuma ba a saba ganin mata suna yinsa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - An gano wata jarumar budurwa mai suna Yemi tana tuka motar tanka a cikin wasu hotuna da @bjyomyom ya wallafa a Instagram.

A kayatattun hotunan wanda Legit.ng ta gani, Yemi ta kasance tsaye kusa da motocin tanka.

Direbar tanka
Mai Kamar Maza: An Gano Budurwa Yar Shekaru 26 Da Ke Tuka Tankar Mai, Hotunanta Sun Yadu Hoto: @bjyomyom
Asali: Twitter

Ba kasafai ake ganin mata suna tuka tanka ba

Ana yiwa tukin tanka kallon aikin maza a Najeriya, kuma ganin kace tana yinsa cikin nasara ya kayatar da mutane.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake wallafa hotunan, @bjyomyom ya rubuta:

“Sadu da Yemi matashiya direbar tankar mai mai shekaru 26. Mamallakiyar kwalin karatu wacce ta fara tuka manyan motoci tana da shekaru 21. Ta kasance madubin dubawa ga hazikan matasa.”

Jama’a sun jinjinawa direbar tankar

Wasu masu amfani da shafukan soshiyal midiya wadanda suka ga hotunan ya burge su kuma sun yabawa matashiyar.

Austin @plusadorable ya yi martani:

“Budurwa mai yanci. Wow,wow,wow! Jinjina!

Chibueze Paschal @ChibuezePascha5 ya ce:

“Gaskiya ita din Jaruma ce.”

Musa Sani: Dan Najeriya Mai Shekaru 13 Ya Sake Kera Wata Gadar Sama, Hotunan Sun Yadu

A wani labarin, Musa Sani, dan asalin jihar Borno mai shekaru 13 wanda ya kwaikwayi irin gadar saman Maiduguri ya sake kera wani da ya burge yan Najeriya.

Sabbin hotunan da Onivwo-Omasoro Ali Ovie ya yada a Twitter ya nuna cewa yaron ya sake kera gadar sama mai girma da hanyoyi da dama.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan Arewa: Kamata ya yi Shettima ya hakura da takara da Tinubu saboda dalilai

A cewar wallafar da aka yi a Twitter, yaron ya yi amfani da jar laka da fenti wajen cimma wannan aiki da ya ja hankalin mutane da dama kuma ya burge su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng