An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

  • An karrama Misis Onokpite Agbaduta, uwa daya tamkar da dubu wacce ta zama direba don kula da yaranta
  • Gidauniyar Alice Ajisafe ce ta nemo Agbaduta sannan ta karramata bayan labarinta ya karade ko’ina
  • Legit.ng ta zanta da matar mai shekaru 59 kuma ta ce yakamata labarinta ya karfafawa sauran mata gwiwa

Bayan fice da labarinta ya yi a yanar gizo, Gidauniyar Alice Ajisafe ta karrama Misis Onokpite Agbaduta, wacce ke aiki a matsayin direbar bas.

Labarin bajinta na wannan mata mai shekaru 59 wacce ke tuka motar haya daga wannan jiha zuwa wata ta burge mutane da dama a shafukan soshiyal midiya.

Direba
An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta Hoto: Daily Trust and peeterv/Getty Images.
Asali: UGC

Labarin kukan kurciya ne

A cewarta, ta zama direbar mota ne bayan rasuwar mijinta wanda ya kwanta dama a shekarar 1991.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

Misis Onokpite wacce ke da yara uku ta yi nasarar daukar nauyin karatunsu har zuwa matakin jami’a duk a cikin wannan sana’a da take yi.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafin Facebook, ta yi godiya ga yaranta a kan yadda suka kasance tare da ita a wannan sana’a da ta zabi yi.

A wata hira da ita, Misis Onokpite ta fadama Legit.ng cewa wadanda suka shirya taron karramata sun ga labarinta ne sannan suka ce ya zama dole duniya ta san da ita baya ga karramawar.

Yaranta sun kasance a wajen don karfafa mata gwiwa yayin da ta karbi lambar yabon.

Kalli wallafarta a kasa:

Gidauniyar Bashir Ahmad Ta Dauki Nauyin Karatun Yarinya Mai Baiwar Lissafi Tun Daga Firamare Har Zuwa Jami’a

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya tarbawa garin wata karamar yarinya yar asalin jihar Kano nono, inda ta samu tallafin karatu kyauta tun daga Firamare har zuwa jami’a.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro

Saratu Dan-Azumi kamar yadda aka bayyana sunanta, ta kasance hazikar yarinya wacce Allah ya yiwa baiwar hada lissafi duk da karancin shekarunta.

Gidauniyar tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya dauki nauyin karatun Saratu bayan ya samu yardar mahaifanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel